Main menu

Pages

MAGANI KYASFI, KO MATSALAR FATA DA KURAJEN JIKI KO FUSKA MAGANIN KYAZBI KO MATSALOLIN FATA KO KURAJEN FATA KO NA JIKI KO NA FUSKA


Kawai za a je Islamic chemist ne a sayi khal tuffa babban kwalba me hoton Apple daya, Man Sim-sim wato man Ridi Dan Misrah banda Dan Nigeria guda 4, Man Hulbah dan Misrah guda 4 sai ka hada man simsim da man hulba gu daya ka gaurayesu, 
Sai a dinga dangwalar Wannan khal tuffa din kana shafe dukkan jikinka musamman inda abin ya shafa da shi, amma zaka yi hakan ne bayan kayi wanka, in abinda ka shafa ya bushe sai ka dakko hadin man nan shima ka shafe jikinka da shi, ka yi haka a kalla tsawon kwana 14 zaka sha mamakin yadda fatarka zata yi Fresh tayi kyau, 
kuma duk kyazbin ma zai mutu, in da wasu kuraje ma duk zasu mutu, inshaaAllahu ko gyara fata ake so a yi ana iya amfani da wannan bayanin Allah ya sa mu dace.


Comments