Main menu

Pages

HK MUSULMAI ZASU CIGABA DA DAUKAR KASKANCI DA CIN ZARAFIN ADDINSU SBD TSARIN NYSC

 


NYSC!!! NYSC!!! NYSC!!!


Shin haka musulman Nigeria za su zauna cikin dawwamammen kaskanci da wulakanci da cin zarafin addinin su a cikin wannan tsari na NYSC!!!


(1) Na ga aboki na ya rubuta cewa an kori mata musulmi guda (4) daga Camp saboda sun sanya Hijaab iya gwiwa a Camp din Minna Niger State.satin da ya gabata 2018 BATCH B kenan da suke cikin Camp a yanzu.
(2) Yanzu wani aboki na ya ke sanar min cewa yau din nan, dazu-dazu a Camp din Imo State wani soja ya ci zarafin wata musulma saboda tasa Dankwali (Head tile), har ya kwace mata I.D CARD.
(3) Haka shekarun baya da suka wuce wani soja a Nassarawa State Camp ya buge wata musulma (Ameera MSSN) ya yi mata dukan tsiya saboda ta sa Hijab ko wani abu makamancin haka.
Akwai dai labarai da yawa wadanda ba boyayyu ba ne ga al'umma dangane da yadda ake cuzgunawa musulmi ake hana su Yancin su na addinin su a harkar NYSC.
Hakika ya kamata a samar da revolution a wannan lamari,kamar yadda Firdausi Amasa ta samar a harkar rantsar da Lauyoyi.
Tun da musulman (Masu fada aji, Shugabanni masu iko a wannan harka) ba su da kishin addini, babu shi a agenda din su, Shugaban NYSC musulmi ne dan garin Kazauren Jihar Jigawa, amma babu ruwan sa da irin wannan lamari, haka nan wadanda suka gabace shi akwai musulmai da yawa daga cikin su, amma su wannan abun ma basu dauke shi a matsayin komai ba.
Musulmi ku tashi ku nemi 'Yancin ku,kada ku bari a lalata muku addini,a wulakanta ku,a ci zarafin addinku.Dokar Kasa ta baku dama,duk abun da za a yi wanda ya ci karo da addinin ku kuna da damar neman Yancin ku.Allah Ya isa tsakanin mu da duk wanda ya kawo mana wannan masifa,Allah wadaran duk mai ikon kawo gyara a wannan harka amma ya yi burus.


Comments