Main menu

Pages

MUHIMMAN ABBWN DA YA KMT KIYI LOKACIN AL'ADA DA BAYAN TA.

 
ABUBUWAN DA YA KAMATA MACE TA KULA DASU LOKACIN DA TAKE JININ AL'ADA


Wajibi ne ga macen da take al'ada ta qara ninka yanda take kula da jikinta kasancewr yanayin da take cikin kan iya jawo mata matsala matuqar bata kula da kanta ba.
Wannan kenan ya hada da canza pad ko tsumma akai akai domin kaucewa cututtuka, da warin jiki da zai dameki ya damu wanda yake tare dake saboda gaskiya akwai matan da basu damu da tsaftace jikinsu ba.
Idan kika tashi canza pad ki hada har da pant🩲 dinki ki wanke gaba daya ko yayi staining ko bai yiba ki canja shi.
Ki kula da inda zaki tsugunna ya kasance tsaftataccen toilet ne, saboda a wannan lokacin kina dan qara budewa saboda jini ya samu ya fita, to in akai rashin sa'a bakya kula sai kiga ba wuya infection ya shiga jikin ki
Kada ki kuskura kiyi tsarki da ruwan sanyi saboda illa ne ga lafiyarki musamman ma a wannan lokacin, gurin yana buqatar ruwan dumi da zai gargasa ki, ke kanki sai kin fi jin dadi, sannan kuma in an fito daga toilet a dinga wanke hannu da sabulu please kada a ringa barinshi haka.
A takaice dai mace ta kula sosai da tsaftar jikinta ciki da waje dan kare kanta da kuma wanda suke tare da ita, 
Dan wasu matan ka zauna dasu sai ka kasa numfashi saboda tsabagen qazanta, jikin mace kaca-kaca ba gyara ko kadan a tare da ita, in anyi magana tace period take sai kuma aka ce miki lokacin period lokacin qazanta ne? mijinki ya dinga qyamatarki saboda qazanta? dan Allah mata ku gyara ko dan lafiyarku ba dan wani ba
Sannan a kiyaye fita musamman da dare saboda Lokacin da mace ke jinin Haila babu tsaro tare da ita, Kowanne Aljani mugu ko mayu ko sihiri zai iya kamata ko yayi tasiri a tare da ita sbd rashin sallah da kuma zubar jini a tare da ita, sbd haka ki kiyaye yawace yawace in kina jini, akwai matan da tsabar wauta har jima'i suke Alhalin suna jini kuma yana haifar da matsaloli iri iri da cututtuka Allah ya kiyayeRIGAKAFIN DA YA KAMATA MACE TAYI LOKACIN DA TAKE CIKIN YIN JININ AL'ADA SABODA KARIYA DAGA SHEDANUN ALJANU KO SIHIRI KO MAYU


Ana son ki nemi Jan muski kina shafawa a hammata kadan kadan, da kuma Naman duwawunki, sannan ba laifi in kina shafa man Habbatussauda ma a jiki shima yana tasiri sosai wajen kariya a wannan lokacin, da kuma ki iya yinsu duka gabadaya.ABUBUWAN DA YA KAMATA MACE TAYI BAYAN TA GAMA JININ AL'ADA'🩸 DA KWANA DAYA


Kamar Yadda ya zo A hadisi cewa Nana Aisha takan bi duk inda jinin ya taba da auduga ta Goggoge da muski ba ta cusa ba, da fatan an gane za a yi hakan kafin ayi wanka, sannan za a sake yi bayan anyi wanka har kwana uku kachal, Sannan ki nemi Zaytu-Lauz Wato Almond Oil


 Danmisrah guda Biyu ki hada da Zatul-Jirjir da safe kafin ki ci komi ki sha chokali biyu, da yamma ma ki sha chokali biyu, hakan zai taimaka miki wajen tsaftar mahaifa da koro duk wani guntun jini da ya makale ko ya daskare a jikinki, 
Sannan zai kara tsaftace mahaifar yadda ya kamata sosai, sai kuma yawaita tsarki da ruwan dumi shima ba adadi ma kam wannan kullum ne da mace me aure da marar aure duk ana son su dinga yawan tsarki da ruwan dumi

Comments