Main menu

Pages

SULHU YA TABBATA TSAKANIN BUA DA DANGOTE

 AN YI SULHU TSAKANIN DANGOTE DA ABDUSSAMMAD BUA


Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da dattawan Kano sun shirya zaman sulhu tsakanin manyan 'yan Kasuwa Najeriya, Aliko Dangote da Abdussammad Isyaka Rabiu.An yi zaman sulhun ne, don kawo karshen zarge-zargen da ake na cewar 'yan kasuwar na takun-saka kan sarrafa sukari.A yayin taron an yi sulhu tare da watsi da zargin da ake na Dangote na hura wa shugaban kamfanin BUA, Abdussammad Isyaka Rabiu wuta kan kara farashin kayansa, gabannin karatowar watan Ramadan.Taron ya samu halartar manyan dattawa da suka hada da; Alhaji Aminu Alhassan Dantata, Ministan Kasuwanci da Masana'antu Niyi Adebayo, wakilan Sarkin Kano, Sarkin Dawaki Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, shugaban NEPZA Adamu Fanda, shugaban Majalisar Limaman Masallatan Juma'a na jihar Kano Sheikh Nasir Adam.Kazalika, gwamnan Kano, Ganduje da Dantata, sun gargadi manyan 'yan kasuwar game da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, inda suka shawarce su da maida hankali wajen fardado da shi.Dangote da Abdussammad, sun yi alkawarin kaucewa duk wani abu da zai kawo sabani a tsakaninsu tare da yin barazanar jefa Najeriya wani mawuyacin hali a dalilinsu.

Comments