Main menu

Pages

MUHIMMAN BAYANI GAME DA HAIHUWA

  



   BAYANI AKAN  HAIHUWA DA BAYAN HAIHUWA


A lissafin masana kiwon lafiya ana kyautata zaton mace mai ciki za ta haihu ne tsakanin makonni 38 zuwa 42.


Da zaran mace tashi alamomin ga makonnin nan zata fara jin wadannan alamomin (alamomin nakuda)

1 Yawan fitsari

2 Daurewar mara

 3 Ciwon mara

 4 Ciwon baya

 5 Nauyin Ciki

6 fitar da wani Abu mai kamar majina a bakin mahaifa.



A duk lokocin da kika fara samun wadannan alamomi kije asibity kiyi magana da ungozoman ki akan nakuda da kuma hanyoyin da za ki bi ki haihu lami lafiya, da kuma me ya kamata ki tanada kafin lokacin haihuwar tazo.



Sabida haihuwar gida nada hatsari sosai musamman ga wadannan mata :

1- Mace mai ciki na farko

2- Mace mai ciki na shidda zuwa gaba.

3- Idan kwanciyar yaro baiyi daidai ba.

4- Wacce take samun alamun kunburin kafa.

5- Idan ana tsammanin tagwaye ne.

6- Idan mace ta taba samun zubar jini bayan haihuwa.

7- Idan mace an taba yi mata tiyata na haihuwa.

8- Macen da bata da tsawo (gajeriya)

9- Mace mai rashin jini.

10- Matar da take samun zubar jini.


Sabida haka muna kira ga dukkanin mata kada suyi gangacin haihuwa a gida domin tana da hatsari sosai.


ABIN LURA BAYAN HAIHUWA:

1- Nan da nan a bawa jariri nonon mamansa na farko. Domin tana kiyaye lafiyar jariri.

2- Kada a bawa jariri komai bayan haihu wa da suanan magani, ko saka Masa wani Abu a cibiya.

3- A bada Jariri ayi masa riga kafi da zaran an ba shi nono.

Comments