Main menu

Pages

                       
                          PIZZA

Kayan Hadi

• Filawa

• Gishiri

• Yis

• Man zaitun

• Manshanun kanti (Cheese)

• Mayonnaise

• Kayan kamshi

• Tumatir da farar albasa da koren tattasai

• Tsokar\ kaza

YADDA AKE WANNAN HADIN

 

Da farko za a jika yis da ruwan dumi kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun. Sannan sai ki kara filawa a cikin wannan ruwan yis din ki kwaba har sai ya yi tauri. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko laushi sosai sai ki kara fulawa don yayi tauri. Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30. Idan ya hau (kumbura) sai ki sami farantin gashi ki juye filawar a ciki sannan ki sanya a cikin oben ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar. Ana sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai kanana. Sai ki koma wurin fulawarki ki duba idan ta gasu sai ki fito da ita.

 


Sannan ki dauko kayan tumatir din da kika yanka sai ki zuzzuba akai da dan garin kayan kamshi ki barbada. Sai ki sami tsokar naman kazarki da kika yanka kanana tare ki zuzzuba akai. Sannan sai ki kawo mayonnaise ki yaryada akai. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease). Sanann ki mayar cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa. Za ki ji yana kamshi sosai sai ki fito da shi daga ciki shi ke nan Pizza ta yi sai ci.                MIYAR KODA

 

Yadda ake Miyar Koda

Abubuwan hadawa

Koda daidai bukata

Maggi 5

Albasa 1

Attarugu 4

Cittah 2

Tafarnuwa 3

Kori


YADDA AKE HADAWA

Da farko zaki wanke kodarki ki yanka kisa a tukunya, ki yanka albasa ki sa gishiri kadan, da maggi daya ki dora a wuta. Idan ya tafasa sai ki daka attarugu da albasa da tafarnuwa ki zuba ki sa cittah ki zuba ruwa ba mai yawaba sai ki rufe.                      KUNUN AYA

Ingrediants :

Aya

Dabino

Kwakwa

Madarar gari

Ginger

Kananfari

Vanilla ko coconut and banana

 

YADDA AKE HADAWA

Dafarko zaki samu aya mai kyau sai ki jikata tunda safe ko kuma a kwara mata ruwan

Zafi abarta tayi 30min, sai a surfata a turmi.

 

Idan an surfa sai a wanketa tas asa ginger da kananfari da dibino amma sai an cire kwallayon an wanke, da kwakwa itama sai an fere bakin bayan sai ayanka kanana sai akai a markada ko a markada a bulanda.

Idan an markada sai a tace asa madara da sugar da flavour agauraya sai asa a fridge ko asa kankara.                  MIX JUICE

_APPLEj

_CARROT

_LEMON

_CUCUMBER 


Dafarko yar uwa zaki da kankare bayan karas kifitar da dattin,saiki dauko cucumber da apple ki wankesu duka saiki yankasu kanana kizuba ablander kimarkadasu inyayi laushi saiki tace,


kisami kofi daban kiyanka lemon tsami kimatseshi saiki tace akan lemon saiki sa zuma ko dafaffen sugar asa qanqara ko a frij.

Comments