Main menu

Pages

HUKUNCIN SHAN MAGANI GA MACE DON KAR TA SHA AZUMI

 BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA HAILA ?To  amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195.

 Sai dai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa. 

Musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye, Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 


Allah ne mafi sani.


Comments