Main menu

Pages



 YADDA ZA A MAGANCE MAIKON FUSKA DA NA FATA, KAFIN KIYI KWALLIYA YA KAMATA KISAN WACE IRIN FATA GAREKI.

Da farko dai kafin mace tayi kwalliya akwai bukatar natsuwa da kuma lokaci.


Lokacin gudanar da kwalliya daki - daki sannan a tsare don tabbatar da yin kwalliya a natse.


Bayan wannan abu mafi muhimmanci shine kisan yanayin fatarki tun daga launinta zuwa gautsi, tauri ko laushinta.


Wannan zai baki damar sanin abubuwan kwalliya da ya kamata ki harhada wadanda fatarki zata amsa.



Saboda sau da yawa zakaga wasu sunyi kwalliya amma sam kwallyar bata hau fatarsu ba.



Yadda Zaki gane yanayin fatarki.


Fata mai maiko ( oily skin) Zaki ganta ko da yaushe tana da maiko, ko an shafa mai ko ba a shafa ba. Kuma kowane lokaci in an goge Zaki ga maikon yana fitowa. Sannan da anyi kwalliya zata narke ta lalace kamar ba a yi ba, fuska tayi ta kyalli tana naso.



Yadda ake kula da fata mai maiko (oily skin)


Yawaita yin "Facial mask" da danyen kwai, yadda akeyi kuwa shine;



Zaki fasa kwai danye, sai ki cire gwaiduwar ki bar farin kawai, 


Sai ki lullube fuskarki da tissue paper, sai kisa blusher na cikin kayan shafa din nan, ki ringa dangwalo ruwan kwan kina shafawa a saman tissue din dake fuskarki har ko ina na fuskarki ya jike da ruwan kwan.



Zaki barshi minti 10 zuwa 15 sai ki wanke da ruwan dumi. 



Hanya ta biyu na magance maikon fuska ita ce, ki ringa yawan goge fuskarki da lemon zaki ko lemon tsami kafin shafa kayan kwalliya.


Sannan ki samu nikakkiyar shinkafa, ki Kika ta cikin madara, sannan ki shafe dukkan jikinki da ita minti 20 kafin ki shiga wanka.



Ba magance maikon fuska kawai yakeyi ba yana sa taushi da shekin fata. A ranar da kkai wannan hadin kar kiyi wanka da sabulu, kiyi da ruwan dumi ki dirje jikinki wannan hadin da Kika shafa ki tabbatar ya fita.



Hanya ta uku ta magance maikon fuska ko fata shine, duk man da zaki saya ya zamto an rubuta for oily skin only. Ko kuma for all types of skin. 


Kar kiyi la'akari da kyaun sa, ko kamshinsa, ko tsadarsa.



Hanya ta hudu kuma shine, ki busar da bawon lemon zaki, ki dakeshi yayi laushi sosai.



Sai ki kwaba shi da madara, sai ki shafeshi a fuska,  har tsawon mintuna  10 - 15, kafin ki wanke da ruwan sanyi.



A darasi na gaba insha Allah zamuyi bayani yadda ake magance busasshiyar fata, kar ma wannan lokaci da muke ciki na sanyi ko ince hunturu.

Comments