Main menu

Pages

 

TUSHEN MATSALOLIN AURE A YAU DA YADDA ZA A MAGANCE SU


Wadannan abubuwan guda biyar da zan jero sune tushen duk wata matsala da muke fama da ita a gidajen aure a yau. 


Na kawo su ne a takaice, zan Kuma dauke su daya bayan daya nayi bayaninsu sosai da yadda zamu dauki matakin gyara inshaa Allah.


1- Rashin tsoron Allah: Zan fara ne da tsoron Allah saboda shine mabudin dukkan aikin alkhaeri, kuma makullin dukkan sabo da son zuciya. 


A gaskiya yanzu akwai karancin tsoron Allah a cikin al’ummarmu, musamman a zamantakewan aure.


 Idan nace rashin tsoron ba ina nufin rashin ilimi ne ba ko rashi sanin ya kamata, a’a an sani ake take sanin a biyewa so zuciya. 


Mafi yawan matsalolin aure a yau suna samuwa ne daga bin son zuciya da yin abinda aka ga dama sabanin abinda Allah yayi umurni. 


Da dukkan mu mazan da matan za mu ji tsoron Allah muyi biyayya ga tsarin Allah da wallahi matsalolin da muke fama da su da yawa sun yi kaura.2- Rashin sanin muhimmancin aure: Aure shine hanya guda daya tilo ta samar da nagartacciya kuma sahihiyar al’umma, sannan kuma shine kadai hanyar gina kowace irin alaka. 


Amma Maganar gaskiya shine hausawa yanzu da yawa ba mu san muhimmancin aure ba, kawai dai muna fada ne a baki, saboda mun bar abin da yake da muhimmanci mun koma muna rara gefe.


 Abinda muka fi dauka da muhimmanci a sha’anin aure shine hidiman auren da sharholiyar da ake yi yanzu wajen biki. 


iyayen amarya hankoron su me zasu kai ma diyar su ta wuce gori, furnitures da sauran tarkacen da idan suka yi wasa za’a dawo masu dasu tare da diyarsu. 


dalili kuwa taje tana ma miji abinda ta ga dama saboda rashin sanin muhimmancin mijin da auren gaba daya. 


Ango da Amarya kuma sun fi maida hankalin su wajen tsara events din bikin su yanda zasu shiga tsara.


Shi zaman auren a kashin kan shi bamu dauke shi da wani muhimmancin da za’a shirya masa ba, mun dauke shi wani abu na je ka nayi ka, ko wani al’ada da aka saba da shi.


 Mun manta cewa addini ne, kuma ibada ne me girman gaske da yake kunshe da falala me tarin yawa, kuma kamar sauran ibadodi shi ma aure Allah (T) ya tsara mana yanda zai kasance, tun daga neman auren har zaman gidan auren, akwai abubuwa masu muhimmancin gaske da ya kunsa. 


Amma ba sune a gaban mu ba, shiyasa aure yanzu ya zama abinda ya zama, to mun bar umurnin Allah a cikin sa, mun wawaitar da shi, ta ya zamu ga yanda muke so?3- Rashin ilimin zaman aure: Bayan rashin sanin muhimmancin auren sai kuma rashin sanin ilimin auren, wanda Ilimi ne me girma da fadin gaske da ya kamata kowane saurayi da budurwa su samu kafin su yi aure.


 Iyaye na taka muhimmiyar rawa a wannan bangaren musamman iyaye mata, saboda mafi rinjayen tarbiyyan yaranku mazan da matan duk yana hannunku ne. 


kenan ku kuke da alhakin koya musu zamantakewa, da yanda zasu gina gidajen da sune zasu jagoranta a gaba. Kuma hakan ba zai yiwu ba har sai ku ma kun siffantu da sifa me kyau a zamantakewan ku, irin siffan da kuke so ku dora yaran ku akai, 


domin shi yaro yana da kula, abinda ake aikatawa yake gani yafi yi mishi tasiri akan abinda ake fada masa. Ku tarbiyyantar da yaranku cikin so, kauna da tausasawa, ku koya ma yaranku maza yanda zasu zama mazajen wasu, kuma iyayen wasu, yaranku mata su san kan su, su iya kula da kan su a matsayin su na mata, su san hakkokinsu, su san hakkokin mazajen su a kan su, su san yanda zasu fahimci mazajen su, su zauna da miji cikin girmamawa da kyautatawa, su san ya zasu tarbiyyantar da yaran da zasu haifa a gaba.


 Amma yanzu yarinya duk ba zata san wadannan daga wajen mahaifiyar ta ba, illa iyaka za a koya mata girki da gyaran gida ne, sai social media ne da kawaye suke kazagin zakal akan wannan, wanda bai kawo mana wani mafita sai ma rudani, saboda kowa da inda alkalamin sa ya dosa, kowa ya kan rubuta son ran sa ne ya yada.


 Wannan kalubale ne gare ku Iyaye ku tashi tsaye ku dauki ragamar sanar da yaranku Ilimin zamantakewan aure, menene aure, menene a cikin shi, matsalolin shi da kuma hanyar gyara ko kuma ku bar social media da kawaye su bude idon yaranku su raba masu hankali.


4- Rashin fahimtar juna kafin da bayan aure: Fahimtan juna tsakanin masoya ko ma’aurata shi ma abu ne me gayar muhimmanci, yana da fadi sosai, 


sai dai mun fi ba shi ma’anar fahimtan abinda abokan zaman mu suke so da wanda ba sa so kawai. Alhalin zamu iya fassara shi da ma’ana uku zuwa hudu:Na farko: Fahimtar halaye da dabi’un junanku, da yanda zaku magance wanda ba kwa so a tsakanin ku, ko ku koyi zama da su. Misali yawan fushi, tsaurin ra’ayi da sauransu.


Na biyu: Fahimtar junanku ta fannin abinda kuke so da wanda ba kwa so. Misali, abinci, turare, color da sauransu.Na uku: Fahimtar banbancin ra’ayin da ke tsakanin ku da kokarin samun daidaito. Misali banbancin fahimta/akida, son haihuwa da yawa ko rashinsa, ci gaban karatu/aiki bayan aure da sauransu.


Na hudu: fahimtar me yafi so ko tafi so a tattare da ke/kai. Sannan kuma ta wace hanya saurayi/mijinki ke nuna miki so, sannan kuma shi wace hanya yake so a nuna mishi so? 


Kai ma kuma ka fahimci na ta hanyar na nuna maka so da hanyar da tafi karban naka. Wannan yana bukatar bayani sosai zan fadada zuwa gaba inshaa Allah.


Zaku iya fahimtan abubuwa da yawa a cikin wadannan kafin aure, amma wasu sai bayan aure ne zaku fahimci hakikanin su.


 Sannan kuma rashin samun wadannan fahimtan junan yana iya haddasa matsala me girman gaske da zata iya kai wa ga rabuwa, abinda ba ma fata.


5- Rashin kula da lafiya/gyaran jiki: Yanzu muna wani zamani ne da cutuka sun yi yawa sosai, kuma mun sani akwai cutukan da suke da tasiri a zamantakewan aure sosan gaske wanda yanzu suke damun mata da maza duka. 


Matsalan shine bamu damu da mu san su ba, ta yanda idan mun kamu da su zamu nemi magani mu warke, sai mu bar su har sai sun girma sun haddasa mana matsala a zamantakewan auren mu. 


Abinda ya kamata shine tun kafin auren ma saurayi da budurwa su tabbatar sun tsarkake kan su daga duk wata cuta irin wannan, saboda da yawansu suna yaduwa ne, ko ma baku yada ma abokanan zamanku ba, akwai cutarwa sosai wlh. 


Sai ku gani tun ana hakuri har abu yayi girman da zai bata muku zaman aure gaba daya.


Sai kuma gyaran jiki, shi jikin mutum, musanman mace a ko da yaushe yana son gyara ne, kullum jikin ki na samun nakasu ne, kina haihuwa, ke ko ma ba haihuwa ba ya kamata ki saba da gyara jikin ki saboda jikin ki shine jarinki, 


komai na jikin ki kawa ne, an yi shi ne don ya burge me gidan ki ya ja hankalin shi, idan kika bari ya lalace a hankali zaki daina burge shi, ya fara miki wulakanci, saboda haka My dear, kar kiyi wasa da gyaran jiki, tsaftan jiki, kwalliya, ado, kamshi da sauransu.


 Kuma maza ya kamata ku rika kula da tsafta, gayu, ku gyara jikin ku ku ma saboda mu ma mata muna so mu gan ku da kyau da tsafta domin yana kara soyayya.


Allah Yasa mu amfana da wadanan Jan hankali mu taru mu gyara don DOREWAR zaman lafiya natsuwa da kuma samun cikakkiyar lada daga wajen Allah.A kowane lokaci mu ringa kallon aure a fagen ibadah ba al'ada ba. Allah Ya sa mu game. 
Comments