Main menu

PagesA YAU ZAMU KOYA YADDA AKEYIN SINASIR, FANCAKE, FATEAN DOYA DA KUMA BOOMOO.


          SINASIR


Farar shinkafa

Albasa

mai

Gishiri

yeast

powder

nono


Ki samu ki wanke shinkafarki sai ki zuba albaaa da citta kadan ki bayar amarkada maki yayi laushi sosai.


Sai ki buga kullun sosai sannan ki sa yeast da powder ki juya sai kisa arana har ya tashi ki zo ki juya ki zuba nono kofi daya da gishiri ki juya sosai sai ki fara soya shi 


Powder da bugu shine zai sashi laushi sai kuma isarshsn mai wajan suya.
               FANCAKE


Flour 3 cup 

2 egg

3 tblspn vegetables oil

2 cups cold water 

Baking soda 1/2 tspn

sugar 4 spn

Pinch of salt


Ki hade salt flour da baking soda guri daya ki tankade su sai ki ajje


Ki fasa egg da milk da sugar ki kwaba sai ki zuba cold water ki cigaba da juyawa sannan ki zuba flour kisa whisker kita mixing dinsa har ya saki jikinsa 

Sai ki dinga sa oil kadan a kasko kina zuba shi.kamar waina amma low heat yakeso ki tayi har ki gama


Note:kwabin yafi na waina kamar na spring rolls zai kasance

kuma non-stick zaki using.
         

                FATEN DOYA


Doya 

Kayan miya

nama 

Busshen kifi

albasa

Mai

curry

spices 

maggi

alyayyahu


Ki feraye doyarki ki yankata kanana sai ki ajje 

Ki yi blending kayan miyar ki sai ki soya da mai( mixing ja da fari) in ya soyu sai ki zuba ruwan nama da naman ki kara wani ruwan kadan.ya zama rabin tukunyw sai kisa doya kisa maggi,curry,spices ki juya ki rufe tukunyarki 


Bayan minti biyar ki bude kisa busasshen kifi da kika gyara sai ki kuma rufewa idan.ruwan ya fara janyewa sai.ki saka albasa da alayyahu ki juya ki rage wutar ya zama low heat sai daga baya ki kashe shikenan.
            BOOMOO


Boomoo

Attaruhu

albasa

maggi

Spices

tafarnuwa

citta,masoro,

mai

all purpose seasoning


Ki jika gandar ki ta kwana sai.ki wanke ta tas da soson karfe sai.ki sakata atukunya ki dafata ta dahu da baking powder sai ki sauke ki kuma wankewa 


Ki blending attarhu da albasa ki soya su ki zuba ruwa sai ki zuba gandarki 


Ki daka tafarnuwa da masoro sai citta suyi laushi sai.ki sa aciki ki zuba maggi spices all purpose sannan ki rufe ta cigaba da dahuwa amma wutar kadan dan ta dahu sosai.
Comments