Main menu

Pages

 

YADDA ZA'A MAGANCE CIWON BASIR MAI TSIRO.


_Mutane da yawa na fama da irin wannan cuta don haka masu wannan lalura kuyi kokari ku gwada wannan magani 


Basir mai tsiro ciwo ne dake da wuyan sha'ani sauda dama mutane kansha wahala sosai a kansa wasu kance ma ciwon baya warkewa. 


kuma wannan batu ba haka yakeba, domin babu wata cuta daba maganinta saidai wani lokaci kafin sanin maganin za'asha wahala. 


Wannan darasi zai koya maka yadda zaka rabu da wannan cuta ta basir insha Allahu. 



*Abubuwan bukata*


1.Man Tafarnuwa. 

2.Man Habbatus Sauda. 

3.Man Zaituna. 

4.Auduga. 



*Yadda zaa hada*


Zaka hade wannan abubuwa uku wato Man tafarnuwa,  Man Habbatus Sauda, Man Zaitun da muka lissafa  baki daya saika gauraye sosai a cikin kwalba kokuma wani abu mai tsafata. 


Zaka dauki audigarka daka tanada duk lokacin da zaka kwanta saika dangwali wannan magani daka hada da wannan auduga saika sanya shi a dubararka ma'ana zakayi Matsi dashi. 


Zakayi haka har na tsawon sati guda insha Allahu zaku samu lafiya cikin yardar Allah. 


 *Abin Lura:* 

Yayin yin wannan matsi akwai zafi sai an daure, amma in Allah yarda zaa samu lafiya. 




SAHIHIN MAGANIN BASUR MATA DA MAZA


Asamu 

- Garin Habbatus Sauda cokali 3,

- Garin sassaken Dinya cokali 1,

- Garin citta cokali 1,

- Zuma kamar copy karami.


ku zuba ka gauraya ku motse arika shan cokali 2 safe da rana da yamma wato sau uku a rana..


Idan ya tsiro basir din za a iya samun 

- Garin Hulba,

- Bagaruwa da,

- Garin sassaken dinya.

A rika dafawa ana zama acikin ruwan zafin.



MAGANIN BASUR MAI TSIRO III


Ku samu garin Qirfa cokali 3 ku dafa shi tare da ruwa kofi daya, sannan ku rika shansa da zuma.


Sannan ku dafa sassaken 'Dinya ku zabka shi idan yadan huce ku rika zama cikin ruwan maganin me dumi sosai akalla sau biu a rana safe da dare.

Insha Allah za'a dace.



MAGANIN BASUR MAI TSIRO


A samu Garin Habbatus Sauda cokali 3. Garin Teen cokali 3. Garin sassaken Dinya cokali 1, Garin citta cokali guda. A hada su acikin ruwan zuma, sannan a rika shan cokali 2 safe da rana da yamma.


Sannan a samu garin Hulba da bagaruwa da kuma garin sassaken dinya a rika dafawa ana zama acikin ruwan zafin. (ba sha za'ayi ba).


ALLAH YA SA ADACE.

Comments