Main menu

Pages

DAREN DA BAZAN TABA MANTA WA BA


DAREN DA BAZAN TABA IYA MANTAWA BA


Idan aikin gida tayi bansan sannu ba saide kullum burina naga kuskuren ta anan zakaga saurin mitata


Hakanan bansan iya adadin kukanta ba

Haka nake shareta na kwanta bacci na


Saide ita mai tsoron Allah ce koda munyi fada takan bani hakkina


Baxan bata hquri ko lallabi ba saide na juyo da ita wani lokacin tana kuka haka zan karbi hakkina.

Idan ta tashi tun asuba 4am tafara nafila har dai 7am take tashi


Zanji ta lallaba ta tashi don gyara gida da karyawa


Zan tarar da komai


Naji dadi amma girman kai bai barni nace sannu

Haka ni mai rufin asiri ne amma bansan yi mata kyauta ta kudi ba sbda tanada mahaifiya na kasa ganewa zata iya sai mata wani abu


Sbda batada Sana'a aiki kuma daman na hana


Ko canji bana bar mata agida saina kwashe kayana

Tana girmama iyayena

Yan'uwana

Hatta ga jikoki

Mai son kyauta ce Amma batada halin yi

Inko ta samu kudi to tabbas zatayi alkhairi dasu


Tnda na aureta ban damu da yi mata sutura ba gani nake ai tanada na auren mu

 Tana ciwo amma bakina bai taba cewa ya jiki kona damu da hakan ba


Saide naji tanata juyawa amman sbda Mita na da sanin kar raina ya canza haka zata hqura


In kayan aikin abinci ne tace a sayi wani abu gani nakeyi kamar taimakon ta nakeyi


Gashi ni bana son kyautar abinci.....itako mai alkhairi ce

 Idan gaban yan'uwa nane ko magana tamin dakyar nake amsawa


Duk wannan ukuba bata taba kai qarana ga iyayena ko nata ba


Saide naji tana addua cikin sujjada mai kuka


Ni duk gani na yanaga matan waje

Kodai wata zan auro

Na kasa gane ko wacce na auro halina ne mara kyau, yace ranar da bazan manta ba itace


Ta tambayeni zata wunin sallah gidansu......

Na amince mata


Haka ta hada komai nata ta gyara tun dare


Abinci tamin lunch ta ajje taima yaron mu khaleel wanka


Sai naji sallama

 Ashe qanwar tace da addanta suka zo Dan inada mota Amma bazan kaita ba...

Gani nake daukar ta ciki ma alfarma ce


Suka gaidani na amsa..... suka wuce dakinta tafito tace abban khaleel zamu tafi

 Budar bakina nace bazaki jeba da sauri ta dago ta kalleni nace eh


Tayi roqon duniya nace aa haka ta share hawayen ta ....... A tunanina zata fadima yan'uwa ta

na kasa zama nazo bakin kofa naji tana addua kamar haka


Ya Allah nidai ban sabeka wajen hidimar biki naba

Banyi abunda ka Hana na Kidi ko rawa ko hada mata da maxa ba

Sai na labe ji nayi tace adda kuyi hakuri abban khaleel baiji dadi ba


Bazan samu zuwa gida ba haka sukayi addua Allah ya bani lfy suka wuce

.

Na sake binsu naji qanwar ta tace anya ba hanata yayi ba adda


Da shike sun samu tarbiya sai addan tace a'a baijin dadi da kin ganshi..  amman nasan tagane

Na koma daki na tarar tana kuka mai ratsa zuciya tabbas na karaya

Amman ganina sai naga ta tashi na dauka fada zamuyi domin idan ni akaiwa haka tabbas akwai abu


Sai naga ta shiga toilet tadan dade kafin ta fito nasan kuka take


Sai ta fito ta daura sallah aladar tace walaha


Na fita falo domin nima raina ys soso yau Amma girman kai bazai barni na bata hquri ba

Nayi dukkan addua da ka sanar lokacin da akace an daura aure na


.hasbunallahu wa ni'imal wakeel.

Nashiga gidana da sallama da addua


Nayi adduar zama bakin gadona


Duka tana Fadi cikin kuka


Ya Allah ina roqon ka idan na saba maka cikin rashin sani ka yafeni..


Ya Allah karka kama mijina wlh na yafe masa

.

Ina kuka ne domin neman gafarar ka badan fushi dashi ba

Ya Allah nasan shima bazai so kunci naba saide jarrabawa


Ya Allah kasa mijina ya gyara Kayi albarka gareshi da arziqin sa

.

Ya Allah kada ka kamani da rashin kyautawa iyayena bani abunda zan saya musu kona ziyarar cesu saida yardar mijina


Tabbas ranar naji tausayi na tuna duk kunci da take da wulaqanci na Ashe addua take man in tana kuka


Nayi nadama amman girman kai ya jani


Na shirya Zan fita sai na samu tana kwance nace zan fita......


Haka ta daure tamin addua na lura kamar daqyar ta miqe amma na share


Na fice sai tace min inajin zazzabi abban khaleel


Cikin murya mai rauni

Nace Allah ya sauwaqa kisha magani mana nasa kai na wuce


Cikin  dare ina kwance domin  banzo dakinta ba

Ashe wannan ciwon zazzabi yaci karfin ta

Na sameta Kwance


Nace yau bazaki zo dakina bane


Bata amsa ba nace bada ke nake ba a tunani na ko fushi tayi


Haushi ya kamani naje da nufn jawota


Nan naga tashin hankali daren da bazan taba mantawa ba.....sai naga ta fado qasa......na duba da kyau ashe ta rasu tana sallah kan sallaya ta jingina da kujera😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

Comments