Main menu

Pages

AMFANIN ZOGALE GUDA18, DA MUHIMMANCI ALMISKI




AMFANIN ZOGALE GUDA 18 GA DAN ADAM


Ana Bukatar Jama’a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al’umma domin Qaruwa da Juna.


1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).


2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.


3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.


4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.



5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin sauri warkewa.


6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana  maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.


7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.


8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.


9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.


10- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.


11- Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.


12- Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.


13- Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.



14- Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.


15- A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.


16- A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendix).


17- Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.


18- Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.





Muhimmancin Turaren Miski Ga Dan Adam


Shi dai Miski turarene mai kamshi, kamshin kuma mai sa nishadi da annashuwa.


Yana da kyau kwarai da gaske a ce a matsayinki na mace ko da yaushe ya kasance kina da miski a dakinki domin ana so ko yaushe ki rika amfani da shi.


Mun riga mun sani shi kamshi abu ne da ya ke kara dankon soyayya, kuma yake dawwamar da ita, sannan miski yana dauke da sinadarai da dama da suke ba wa farjin mace kariya daga cututtuka, saboda haka ana so kullum mace ta rika amfani da shi.


Kalolinshi guda uku uku ne.


Akwai fari mai kamar madara mai kauri: Shi wannan ba’a sashi a cikin farji, saboda a daskare yake bai fiya narkewa ba, sai dai a shafa shi daga wajen farji.


Akwai fari kal kamar ruwa, kamshinsa kusan daya ne da mai kaurin, sai dai shi ba shida kauri, to shi za’a iya sawa a matsi da shi.


 Tabbas yana taimakawa har a bangaren auratayya, kuma duk sanda mijinki ya ji wannan kamshin ko bakwa tare ta zai tunaki Zai yi sauri sauri ya dawo gida kinga miski yayi amfani kenan.


Akwai jan miski wannan masu fama da matsalan aljanu suke shafashi, domin yana fatattakar aljanu da iznin Allah. Abinda na sani dai idan mai aljanu tana shafa shi in dai an riga an yi mata rukiyya, to suna rabuwa da ita. 


Amma idan ba ayi ba to za ka ga bata san kamshinsa, ba za ta yi amfani da shi ba.


Shi ana shafa shi ne a duk jiki da gabar da ta fi yi wa mai fama da aljanun ciwo. Kun san fa miski asali ya samo yana da kyau kiyi taka-tsantsan wurin amfani da shi, domin ba wai kawai dangwala za ki yi da yatsarki ki saka ba a’a, Za ki nemi ruwan dumi ne ba mai zafi sosai ba, ki je ki kama ruwa da shi, ki wanke wurin sosai, sannan ki samu hankici mai kyau ki goge ko da Tishu. 


Daga nan sai ki samu “Cotton bud” wato abin sosa kunne.


Sai ki dangwalo da shi, sannan ki tura shi a gabanki, ki dan matse kafarki sai ki cire ki jefar. To in sha Allahu ko ‘fant’ dinki kika cire kamshi za ki ji ba Zai yi wari ba. Babu kunya cikin neman ilmi musamman ilmin addini, babban abun kunya a ce mijinki zai kusance ki kuma ya ji farjinki yana wari, haba! wannan ai ba aji.


Zaki iya dafa ganyen magarya in ya huce ki zuba miskin kina kama ruwa da shi. Sannan ana so duk sanda za ki saka ‘pant’ dinki to ki diga miskin a kai duk wasu kwayoyin cuta za su mutu da yardar Allah. Ana kuma shafa miski a jiki ana kuma hada shi a cikin Humra yana kuma taimakawa macen da ta haihu kwarai da gaske. Yana da kyau a ce a matsayinki na mace kar a rasaki da wadanna abubuwan Miski:


Ganyen Magarya

Hulba

Habbatussauda

Man Zaitun

Man Tafarnuwa

Khaltufa

Lalle

Zuma




Comments