Main menu

Pages

KINA KIYAYE WADANNAN ABUBUWAN KUWA, A MATSAYINKI NA MATAR AURE?

 


A Matsayinki Na Matar Aure, Kin Kiyaye Wadannan Abubuwan Kuwa?


Ga wasu abubuwa da ya kamata mu kula da su a cikin zamantakewarmu domin kyautata jin dadin zaman namu.


Yana daga cikin abin da ya dace mu kula da su mu mata a cikin zamantakewa saboda mu sa ni duk abin da muka yi abin koyi ne ga yan baya.



Na farko, yana da kyau Mace ta zama me kawar da kai musamman akan duk wata harkar maigida da bata shafeta ba, ka da Mace ta zama me tsananin zargi ko tuhumar maigida a koda yaushe, wannan zai bashi damar ha’intar ta, ta kowacce fuska. Ki aminta da maigidanki ta yadda zaki samarwa kanki kwanciyar hankali.



Binciken maigida har kullum ina fada ba abu ne me kyau ba, wanda ba wani fa’ida akan hakan. Idan yazo da wani uzuri ki bashi lokaci yadda zaku fahimci juna. Gidan mijinki shi ne duniyarki wanda in kin gyara ya Samar miki da lahirarki. To akan me mata za a dauki rayuwar aure da wasa ta yadda karfi da yaji yake neman ya kaimu ga halaka? 




A yanzu kalilan din mata suka rage da yi wa mazajen su addua, wanda kuma suna bukatar adduar ta kowacce fuska amma ba a yi sai in kuskure ya faru ayi ta samun matsala karshe kuma ba a cika ganin laifin mazan ba sai ta mata to ina riba a yin hakan. Mu sa ni miji ko gidan aure ba wuri ne na yin fito na fito ba sai dai wurine na ibada da neman lahira.




Mata da yawa a yau sun dauki rayuwar aure da wani irin tunani da ke kewaye da rashin yadda, zargi,  tuhuma da sauransu wanda wadannan suke wahalar da rayuwar gaba daya a karshe shaidan ya shigo ya taya dari bisa dari. Yan uwa mata muyi kokari mu zama abin koyi a cikin alumma ta ya yadda zamu zama abin kwatance ko ba ma raye.



A karshe mu sa ni mazaje  na bukatar adduoinmu fiye da bincike ko tuhumarmu. Allah yasa mu gyara.

Comments