Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI DALILIN KAMA ADO GWANJA DA HANA SA YIN WAKA

 




Cikakken Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Haramtawa Ado Gwanja Yin Waƙa, Bayan Kama Shi


Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a A'isha Mahmud ta bada umarnin a kamo mata mawaƙi Ado Isa Gwanja.



Idon Mikiya ta rawaito Kotun ta kuma haramta masa waƙa har sai 'yan sanda sun kammala bincike a kansa.



Idan za’a iya tunawa a bara lokacin da mawaƙin yayi wata waƙa mai suna “WAR” zauran malaman Kano sun shigar da shi ƙara a kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi ta hannun lauya Barr. Sulaiman Gandu, saboda a cewar su waƙar akwai kalaman batsa a cikinta kuma zata iya ɓata tarbiyyar yara a Kano.



A wancan lokacin kotun ta bada izini a kamo mawaƙi ado Gwanja, amma sai ya garzaya babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba biyar ya kuma karɓo takardar da ta hana kotun ta kama shi a wancan lokacin.



A zaman ta na wannan rana kotun ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a A'isha Mahmoud ta bada umarnin a kama Ado Gwanja, sannan ta ce ta haramta masa yin kowacce irin waƙa har sai 'yan sanda sun kammala bincike kan zargin da malaman Kano suka yi masa.



Haka zalika kotun ta ce ta haramtawa Ado Gwanja zuwa gidan biki don yin waƙa, sannan kuma ta hana wani ko wata ya hau wakar sa a dandalin sada zumunta.



Kotun ta ce duk wanda ya hau waƙar kafin a kammala wannan Shari’ar to su sani sun karya doka kuma kotu zata sa a Kamo su. Idon Mikiya

Comments