Ingantaccen Gyaran Breast, ya tashi kyam kyam kamar na budurwan.
A wannan lokaci za mu yi bayani dalla-dalla kan yadda mace za ta gyara nononta, ya dawo kamar na budurwa, kwarai kuwa, wannan ba wani abu ne mai wahala ba. Da zarar kin yi amfani da wanna hadin, nononki zai koma ya tsaya cak kamar na budurwa.
Ba tare da bata lokaci ba, za mu kawo mu ku yadda za ku yi wadannan hade-hade cikin sauki. Da fatan a sha karatu lafiya, da fatan kuma bayan an karanta za a jarraba.
1. Gyaran Nono.
Wannan wani hadi ne da masana kiwon lafiya su ka samar bayan gudanar da zuzzurfan bincike. Kuma babban abin farin ciki game da wanan hadi, baya ga saukin hadawar sa, an jarraba an ga fa'idarsa, sannan ba shi da wata illa ga lafiyarmu, saboda dukkan kayan hadin dangogin abincin da mu ke ci yau da kullum ne.
Abubuwan Da Ake Bukata:
a. Hulba.
b. Gyada.
c. Alkama
d. Ridi.
e. Shinkafa.
f. Karas.
Wadannan kayan abinci ake bukata mace ta tanada. Abin da za ta yi shine, ta samu garinsu. Abin nufi kamar shinkafa, sai ta gyara ta sosai ta daka ko nika yadda za ta samu garinta. Haka za ta yi wa gyada, ridi, da alkama. Ita kuwa hulba sai ta sayo garinta, shi kuma karas sai ta shanya shi ya bushe sannan ta samu garinsa.
Bayan ta sami garin wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraye, daga nan ta adana su a mazubi mai tsafta, kuma mai murfi.
Yadda za ta yi amfani da wannan hadin gyaran nono shine, za ta sami madara 'Peak' idan son samu ne, ta ke zuba wa ta sha a kullum. Za ta sha mamaki matukar ta juri amfani da wannan hadin gyaran nono, domin kuwa nononta zai dawo tamkar na budurwa, da iznin Allah.
Comments
Post a Comment