Main menu

Pages

HADIN MATAN AURE, GA MATAR DA KE FAMA DA KARANCIN NI'IMA

 



Ingantaccen Hadin na Matan Aure, ga matar da tasan tana da karancin Ni'ima.

Kamar yadda mu ka sani ana samun mata da kan yi kukan rashin ni'ima, wanda hakan kan hana jin dadin jima'i tsakanin ma'aurata, sannan ya haifar da rashin gamsuwa tsakaninsu. Idan har kina fama da wannan matsala ko matar ka na fama da matsalar rashin ni'ima, sai ka karanta ka fada ma ta don ta hada.




Kayan Hadin Da Ake Bukata:

a. Ruwan Kankana, Kofi 1 

b. Garin Dabino, babban cokali 3

c. Zuma, babban cokali 3

d. Madarar "Peak" rabin gwangwani.


Idan amarya ko uwargida ta tanadi wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, abin da za ta yi shine, za ta cakuda garin dabinonta da ruwan kankana da zuma, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sai ta zuba cikin madararta, ta ke sha, da iznin Allah matsalarta za ta kau. Shi wannan hadin namiji ma zai iya amfani da shi.




Hadi na Biyu

Shi kuma wannan hadin, baya ga karin ni'ima da mace za ta samu, hakanan zai kara mata dadi yadda za ta iya gamsar da mijinta.


Kayan Hadin Da AKe Bukata:

a. Aya, babban cokali 5

b. Ridi, babban cokali 5

c. Cikwi, babban cokali 3


Yadda mace za ta yi wannan hadi shine, tun da farko za ta gyara ayarta, sannan ta soya ta, bayan haka sai ta daka ayar don ta samu garinta. Shi kuma ridi bayan ta gyara shi ta cire duk wani datti da ke cikinsa, sai ta nika shi don samun garinsa.

 Hakanan, shi ma cikwi za ta daka shi ne don samu garinsa.



Bayan ta samu garin wadannan abubuwa 3 da aka zayyana a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraya su, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sannan ta adana a mazubinta mai kyau.


Abu na gaba shine, ta samu madara ko nonon shanu mai kyau, sai ta ke zuba karamin cokali 2 cikin nonon ko madarar, ta ke sha safe da yamma a kowanne yini. Samun ni'ima da gamsuwa yayin jima'i ba sai an fada ba.

Comments