Da alama Mutuwar Darakta Aminu S Bono zata zamo shiriya ga wasu 'yan Kannywood.
Da alamu dai wannan mutuwa da ta fado kwatsam a masana'antar Kannywood tagirgiza mutane da yawa Wanda mutane da dama jikinsu yayi sanyi sun fara gane cewa Duniyar ba wajen da za a shimfida tabarma a zauna har a mike kafafu bane.
Wannan mutuwa ba 'yan film kawai ta girgiza ba, har ma da mutane na cikin gari wadanda suka San shi marigayin da 'yan socal media.
A cikin hakane Jarumi Tijjani Asase Wanda Yana daya daga cikin wadanda aka fahimci wannan mutuwa ba karamin dukansa tayi ba yayi ma fitacciyar 'yar TikTok din nan wato Murja Ibrahim Kunya wa'azi ko ince nasiha.
Inda itama din dai alamu suka nuna wannan mutuwar ta sanya tayi laushi daga dukkan fitsarar da ta saba yi a kafafen ta na sada zumunta. Muna fatan wannan taushin da shiga hankali da nadama da kowa yayi ya dore a bisa.
Kowa ya canza rayuwarsa daga abu mara kyau zuwa yin na Kwarai don Duniyar dai kullum gudu take kwanakinmu na karewa Muna kusantar kabari. Allah Ya shiryemu Ya shiryi dukkan musulmai baki daya bisa tafarki Mai kyau. Ga nasiha kuji da kunnenku.
Comments
Post a Comment