Shahararren Furodusa Abdul Smart Mai kwashewa, Ya siyawa Iyalan Marigayi Aminu S Bono Katafaren gida.
Allah Sarki, rayuwa haka take, in kana Raye baka San Waye zai duba bayanka ba idan ka mutu. Kamar dai yanda muka sani shine a makon da ta gabata ne Allah Ya dauki ran shahararren Darakta Aminu S Bono.
Inda rasuwarsa tayi tambari ta watsu a ko Ina aka jita cikin dan kankanin lokaci. Kuma ta taba zukatan mutane da dama, kar ma masana'antar ta Kannywood ta jijjiga da wannan rasuwa ta Darakta.
Muna fatan Allah Ya yafe masa dukkan kurakuransa da musulmai baki daya. To bayan wannan rasuwar ne fa abokan aiki ' Yan amana Wanda suke tare dashi marigayin suka yunkuro wajen talkafawa Iyalan namacin.
Inda Furodusa Abdul Amart ya sayi Wani dankareren gida a nan cikin unguwar tasu marigayin wato dandago inda ya mallaka wannan gida ga Iyalan Marigayi Aminu S Bono. Allah Ya Saka masa da Alkhairi Ya amfani bayanza Shima.
Bayan wannan tagomashi daga Furodusa Abdul Amart Kuma sai ga shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, Shima yazo da tawagarsa wajen yima Iyalan namacin gaisuwa, inda Shima a nan take yace ya dauke nauyin karatun 'ya'yan marigayin har su kammala dukkan karatunsu.
To Muna fatan Allah Ya bashi ikon sauke wannan babban nauyi da ta daukarwa kansa. Ga zahiri kuji ku gani a wannan video dake kasa.
Comments
Post a Comment