Main menu

Pages

YANDA ZA AYI AMFANI DA DANYEN KWAI WAJEN MAGANCE KURAJEN FUSKA
Yanda za ayi amfani da danyen Kwai wajen magance kurajen fuska.

kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuska. Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.


Abubuwan da za a bukata:

• Kwano/mazubi biyu:

• kwai daya:

• Takardar ‘tissue’ daya:A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.Yanda za a yi hadin:

•A fasa kwai sai a cire gwaiduwar.

•A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.

• Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.

• A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu.

• A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan?

•Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska.

• Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar.

• Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.Muhimman amfani guda 5 da ɗanyen ƙwai ke da shi ga fuskar dan Adam:

Masana sun bayyana wasu kwararan amfani da danyen kwai ke da shi ga lafiyar dan Adam, musamman wajen gyaran fuska, tare da kare fuskar daga matsalar kuraje.

1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin.

2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska.

3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje.

4- Danyen kwai na kara ma fuska haske.

5- Ruwan kai na rage kumburin idanu.


Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.


Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.


Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.

Comments