Main menu

Pages

MUHIMMAN SHAWARWARI GUDA SHA HUDU DA DUK MATAR DA TA RIKESU ZATA MALLAKE ZUCIYAR MIJINTA

 Muhimman shawarwari guda Sha hudu da duk matar da ta yi amfani dasu zata mallake zuciyar mijinta cikin sauki.

In kina son ki shawo kan wuta ko ki kashe ta gaba daya ba wata wutar za ki kara mata ba, nemo ruwa mai sanyi ki kwara mata ki sa ido ki gani in za ta ci gaba da habaka, haka namiji ya ke. Ga wasu shawarwari a kan yadda za mallaki mijin ki.


 

- Namiji bai son a ce kina ba shi umurni, bare a ce kina yi masa nasiha, duk kuwa da cewa yana bukatar nasihar a zahiri, don haka in kina bukatar zuwa wani wuri kar ki ce masa “Zani wuri kaza” ki saka ta a sigar tambaya “Ina son na tambaye ka ne, dama ina so zuwa wuri kaza ne” ko in kina bukatar wani abu kar ki ce “Ka ba ni kaza zan yi kaza” ki zabi lafazin da za ki yi aiki da shi, kamar ki ce “Muna bukatar abu kaza ko za a sayo ne?” Da duk irin lafazin da ke nuna girmamawa da bukatar abin a wurinsa, wata gatsar take fadi, har ma ta kara da cewa “In ba haka ba sai dai a zauna haka”.


 

 

- In kuma dawowa gida ya yi, tarbe shi ku shigo tare, in yana rike da wani abin, karba masa, sai dai in ya nuna ba ya so, kamar jakar kudi da wasu abubuwa da suke bukatar sirri, kar ki yi irin abin da wasu matan suke yi, wadanda ko matsawa daga inda suke ba sa yi, sai dai su ce “Sannu da zuwa!”.
- In kuwa ya fadi maganar da kike ganin cewa kuskure ce kar ki ce ba haka ba, ki jinjina wa tunaninsa ki bar shi haka, daga baya ki dawo da ita ta wata sigar ki ba shi shawara a kai yadda ba zai fahimci cewa fito na fito kike yi da fahimtarsa ba.
- In kuma ya yi miki ba dai-dai ba kar ki kullace shi, bare har ki ce za ki rama, yafe masa, wata rana zai kyautata miki, namiji ne.

 


- Duk kyautar da ya yi miki ko da ba ki bukatarta, ki nuna masa godiyarki tamkar ba abin da kike so kamarta, daga baya bayan ya manta ki nuna masa wata wace ta fi wannan, don kar ya kara kawo miki ta farko.

 


- In za ku shiga wuri tare ki dan yi baya shi ya fara yin gaba, sai in shi ne ya ba ki damar ki wuce.

 


- In yana karanto miki matsalolin da ake ciki, ki zabi kalmomin da za ki rika karfafa masa gwiwa, ki rika yaba wa irin kokarin da yake yi duk da matsalolin da yake fadi.

 


 

- Kar ki yarda gardama ta rika hada ku, ba ta karewa da kyau, in ya ja ki sake, shi da kansa zai gano bai yi dai-dai ba, wasu mazan su kan ba da hakuri, wasu kuma sai dai su yi ta janki da wasa ko su yi miki kyautar da ba su yi niyya ba.

 


- In kika ba shi shawara bai dauka ba daga baya abin ya cabe masa kar ki ce “Ai dama na gaya maka” ki nuna masa damuwarki.

 


- In kika roke shi wani abin ya ce ba shi da shi kar ki nuna rashin jin dadinki, yabe shi ki ce “Ai kai mai yi ne, tun da ka ce babu wallahi na san babu ne, amma Allah ba zai barka haka ba zai kawo in sha Allah”.

 


- In ya kawo miki matsalolin ‘yan uwansa ki nuna damuwarki, kar ki kare su kar ki zarge su, sai ya gama ki yaba masa a kan hakurin da yake yi da su, ki karfafa masa gwiwa, ko da kuwa kin san ba wani abin da yake yi na a zo a gani.

- In zai fita ki raka shi har bakin kofa.

 

- Ki tabbatar ya sa kaya masu kyau, ki goge masa takalmansa.

Comments