Main menu

Pages

FA'DODIN DAKE TATTARE DA SURATUL NASR DA SHARHI A KANTA

 Fa'dodin dake tattare da Suratul Nasr da sharhi a kan ta.


1. Taimakon Allah yana zuwa ga bawa ne lokacin da Allah ya so. Kuma ba wanda ya isa ya karkatar da taimakon Allah ga bawa. 


2. Dukkan wani taimakon Allah ga bawa budi ne na wasu sababbin qofofin alheri wanda shi ma bawan ba lallai ya fahimta ba. 


3. Idan Allah yana son bawa sai yayi amfani dashi wajen daukaka addininsa. Shi ma bawan ya zama ci gaban addini shi ne babban burinsa. 


4. Yawan maimaita (Subhanallah, Alhamdulillah, Astagfirullah wa atubu ilayhi) babbar hanya ce ta samun taimakon Allah a rayuwa da kuma babban budi. 


5. Idan shekaru su ka fara jaa ba abun da yafi kamata kamar yawan tasbihi da zikiri da qoqarin kauce ma sabon zubin adashen zunubai.


6. Duk lokacin da jikinka yayi rauni akan ibadar da take buqatar qarfin jiki toh kar ka bari a rasa samun ibadar furuci (ambaton Allah). 


7. Nasara ko daukakar da ka samu ba dabararka ko basirarka ba ce ta kai ka. Duk taimako ne daga Allah; Don haka qara zubewa da runsunawa a gaban mahaliccinka. 

Comments