Main menu

Pages

AMFANIN TAURA GUDA SHA BAKWAI DA YANDA ZA A SARRAFA TA WAJEN MAGANCE CUTUKA

 Yanda za ayi amfani da Taura wajen magance matsaloli da cutuka har guda Sha bakwai (17).

A watsa Wannan sako domin Yan uwa su amfana


Wannan Dan bishiya mai suna taura yana da zaqi da dan bauri kadan wanda baurin nashi baya hana a ci shi, zaqin nashi ba ya da illa.

1- Yana maganin cutukan daji waton cancer a turance.


2- Macen da take samun ciki yana yawan 6arewa waton miscarriage sai ta nemi wannan tauran ta yawaita ci akai akai.


3- Yana maganin tarin asma sai a jiqa shi a cikin ruwan zafi ana sha da safe.

4- Yana rage radadin zafin naquda 

5- Yana maganin kumburin ciki

6- Yana karawa hanta da qoda lafiya.


7- Masu fama da sickle cells waton sicklers su dinga shan shayin taura. Za su samu saukin wannan ciwon sosai.


8- Macen da naquda tai yiwa nauyi a nemi garin taura a yi shayi a bata ta sha insha Allahu cikin lokaci zata haihu.


9- Maccen da ta haihu ya zamo bata da ruwan nono ta dinga cin taura.


10- Mata masu son samun cikakkar sha'awa su dina cin taura.


11- Mai fama da yawan mantuwa ya dinga cin taura zaiga abun mamaki.


12- Mai fama da karamcin bacci ya nemi garin taura ya dinga jiqawa a ruwa yana sha zai ga biyan bukata Insha Allah 


13- Mai fama da hauhawan jini ya maida taura abuncin shi a kai akai zai yi mamaki.


14- Mai ciwon zuciya da jin quna a kan murfin zuciya ya dinga shan shayin taura.


15- Mai fama da tsananin damuwa na kwakwalwa waton depression ya dinga shan taura.


16- Namijin da yake da karamcin ruwan maniyi wanda ba su kai mil 4 zuwa 5 ya zanka cin taura.

17- Yana sanya cin abinci (natural appetizer)


Kunga tauran nan da kuke gani tana da magunguna sosai a cikin shi.

Allah mun gode maka da kamana ni ima da tsirrai irin Wannan masu albarka


A turawa Yan uwa su amfana


Comments