Main menu

Pages

HANYOYI SHA UKU DA ZA A BI WAJEN AMFANI DA NONON RAKUMI DA FITSARIN SA

 



Yanda za ayi amfani da Nonon Rakumi da Fitsarinsa wajen Maganin wadannan cutuka guda Sha uku (13)


1- Ciwon Sugar 

Mai fama da larurar ciwon suga sai a samo: -

a) Nonon Raƙumi kofi daya.

b) Tirmis Baladi, cikin ƙaramin cokali

c) Garin Hulba, karamin cokali

d) Hubuwbul liƙah  ƙaramin cokali

e) Markadadden bitter lemon ƙaramin cokali.


Sai a kaɗa su a cikin nonon, sai a sha kofi daya da safe kofi daya da yamma tun kafin a ci abinci da awa daya, ma'ana idan an sha maganin sai an samu awa đaya a tsakani sannan za a ci wani abu.



2- Ciwon Daji (Cancer)

Wanda yake da wani ciwo da ya shafi cancer to sai ya yi kokarin jarraba wannan maganin:  

Zai rika shan kofi daya na nonon rakumi da safe da yamma amma tun kafin ya ci wani abu da awa daya. Ma'ana, ba zai ci wani abu ba zai sha maganin. Idan kuma ya sha maganin to sai ya samu awa daya a tsakani, sannan zai ci wani abu. 



Za a yi haka a jere ba fashi tsawon kwana arba'in da biyar. Sannan duk sanda ya sha wannan nonon to zai sha shayin lipton ba madara cikin babban kofi tare da rabin kofi na fitsarin rakumi sai ya gauraya ya rika sha tsawon adadin kwanakin. Sannan shi kansa fitsarin rakumin idan an tafasa shi da ruwa ana yin shayin lipton ba madara ana sha, to magani ne sadidan


3- Cutar Sanyi (Infection)

Idan mutum yana fama da ciwon sanyi, to sai ya yi kokarin hada wadannan mahađin, insha Allahu zai fitsarar da sanyin da yake takura masa a jikinsa.

a)Nonon Raƙumi kofi daya

b) Kanunfari karamin cokali

c) Irƙu Dahab, ƙaramin cokali.



To sai ya hada ya sha kofi daya da safe, tun kafin ya ci wani abu. Sannan kofi daya da yamma, kofi daya da da dare. Sharaɗi shi ne, duk sanda aka sha ba za a ci komai ba sai an samu awa daya da rabi (1/2)hrs) a tsakani sannan za a ci wani abu.



4- Fitar Farin ruwa Mai wari daga al'aura

Sanyi na iya sanya mace ta rika fitar da wani ruwa mai wari, to maganin wannan matsala shi ne, sai ta samu fitsarin rakumi mai dama sai ta tafasa shi, sai ta rika shiga cikin ruwan tana zama a ciki zuwa rabin awa, sannan ta fito. Za ta rika yin haka sau daya a rana, tsawo satin daya. 



5- Matsalar rashin fitar Jinin Al'adah 

Sai ta samu madarar nonon rakumi ta sha kofi daya da safe kofi daya da yamma, to in sha Allahu za ta samu saukin lamarin.




6- Matsalar Kurajen fuska (Pimples)

Duk wanda kurajen pimples suka dame shi suka 6ata masa fuska da fata, to sai ya samu madarar nonon rakumi ya riƙa shafawa a kai, sannan kuma yana shan kofi daya da safe da yamma, tsawon sati biyu. To insha Allahu fatarsa za ta yi kyau, duk wasu bakaken kuraje masu fesowa a jiki za su bace su warke, fata za ta yi kyau da haske.



7- Kaikayin Fata;

Duk wanda yake fama da soshe-soshen fata, da karce-karcen fata, to, sai ya yi kokarin hada wadannan mahadan:

a) Nonon Raƙumi

b) Hububul liƙahu

c) Fitsarin Rakumi 

Da farko kullum zai sha nonon rakumi kofi uku tare da Hububul Lika'hu karamin cokali a rana daya, safe da yamma da daddare, to amma tun kafin a ciwa ni abu ake sha. In ma an sha sai an samu rabi nawa a tsakanı, sannan za a ci wani abu.



To, bayan ya sha wannan hadin, sai ya samu fitsarin rakumi tare da man zaitun ya hada waje daya ya rika shafawa a jikinsa sau uku a rana.



8- Zafin Fitsari 

Wanda yake fama da ciwon fitsari wato yana fitsari da kyar, wani lokaci yana jin kamar ana kona gabansa, to sai ya yi amfani da fujul wato ya tafasa shi a cikin madarar Nonon Raƙumi yana ci da safe tun kafin ya ci wani abu.

Abu na biyu mutum zai iya amfani da wadannan mahaɗan:

a) Nonon rakumi kofi daya

b) Shammar karamin cokali

c) Halful Barri, ƙaramin cokali



Da farko idan an samu kofi daya na nonon rakumi to sai a zuba karamin cokali na garin Shammar sai a shanye shi sai kuma karamin cokali na garin Halful Barri shi kuma tafasa shi za a yi a ruwa a rika sha. Za a rika yin haka sau uku a rana amma sai anci abinci za a rika sha kafin ya ci wani abu.



9- Fitsarin Jini

Mahadan su ne:-

a) Nonon Raƙumi

b) Kanin fari karamin cokali

c) Irƙu Dahabu rabin karamin cokali

 Sai a zuba su a cikin nono a juya a sha safe da yamma da daddare tun kafin a ci wani abu, idan kuma an sha maganin to kar a ci wani abu a lokacin har sai an samu rabin awa ½hr.



  10-  Ciwon Shawara

Mai ciwon shawara sai ya lazimci shan ruwa kofi daya da safe tun kafin ya ci wani abu, sannan kuma sai ya sha Nonon Raƙumi kofi daya tare da cin kayan marmari kamar su ayaba gwanda, mangwaro tufa, da dai sauransu



11- Domin samun Kwarin Qashi

Sai a samu wadannan mahadan:

a) Nonon rakumi

b) Fitsarin rakumi

c) Man Kafur

d) Man Na'a-na'a.


Da farko duk sanda ake cin abinci safe da rana da na dare, to sai a sha kofi daya na nonon rakumi, sannan kuma sai a samu fitsarin rakumi sai a zuba man kafur da man Na'a-na'a, sai a juya shi sosai a riƙa shafe gaba dayan jiki da shi. Za a yi haka sau uku a yini.



12- Raunin Ji na kunne 

Mai fama da raunin ji na kunne, to sai ya yi amfani da auduga mai kyau sai ya jika ta da fitsarin rakumi, sai ya sa audugar a kunnuwansa tun daga yamma har zuwa wayewar gari, sai ya cire. To insha Allahu zai ji yadda kunnensa zai kasance dangane da ji sosai.



13- Maganin daskarewan Jini

Mai fama da matsalar daskarewar jini, sai a samu;

a) Nonon Raƙumi kofi ɗaya

b) Garin Habbur Rashad karamin cokali

c) Bizru Kattan, wanda aka daka shi, karamin cokali.

d) Garin citta mai laushi, karamin cokali

e) Hubbu Likahu karamin cokali.


 Da farko idan aka samu nonon, to sai a zuba wadannan mahadan a ciki, sai a sha kofi đaya da safe tun kafin a ci wani abu, sannan bayan an sha za a samu kamar rabin awa, sannan za a iya cin wani abu. Haka ma da yamma za a sha bayan an sha a sami rabin awa sannan a ci wani abu.

Comments