Amfanin Miyar Kuka A Jikin Dan Adam.
Kuka bishiya ce mai tsayi da take da ganye launin kore tana girma a kasashe da dama a nahiyar Afrika inda kasar Senegal ta kasance gaba a cikin sahun jerin kasashen dake noma ta inda har fitar da ita suke yi su sayar ga wasu kasashe. A jihohin Arewacin Nijeriya, yankin Zuru dake a jihar Kebbi na daga cikin manyan wuraren dake noman kuka inda ko bayan amfanin da suke yi da ita har fitar da ita suke yi suna sayarwa.
Allah ya horewa kasashen mu bishiyoyi masu fa’ida da muke amfani da su a matsayin abinci alhali kuma magani ne na musamman.
Kamin masana kimiyya su yi nazarin alfanon dake a cikin miyar kuka, an dauki lokaci mai tsawo ana amfani da ita a kasashe da dama a matsayin miya wacce aka fi sani kuma aka fi gaskatawa.
Sai kimiyya ta zo ta bada nata gudummuwa wacce ta yi bayani daki-daki dan gane da dimbin amfanin miyar kuka. Ga kadan daga cikin su:
Miyar kuka tana kunshe da muhimman sinadirai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya. Akwai sinadiran carbohydrate masu baiwa jikin dan-Adam kuzari, akwai natural sugars wacce ba ta da wani illa ko lahani ga jikin ko wane mutum, akwai proteins wadanda sune ke gina jiki, akwai carotenes, riboflabin, Bit-C, Minerals, potassium, iron, magnesium, manganese, phosphorus, zinc, calcium, glutamic, catechins, tertrate, rhamnose, glutamic acid da sauransu.
Miyar kuka tana taimakawa sosai ga mai fama da basir, tana maganin wannan ciwon musamman ga wanda basir ya tabawa hanjin ciki inda zai haifarda todins na kwayar cutar bacteria ta E.coli wanda ciwon ciki zai addabi mutum da yawan tusa mai wari da kumburin ciki.
Miyar kuka na dauke da sinadiran Iron masu kara yawan jini fiye da wadanda ke a cikin nama. Kenan shan miyan kuka indai sinadiran Iron ake nema yafi cin nama.
Miyar kuka na dauke da sinadirran Bitamin C masu yawan gaske dan haka idan ana neman sinadiran bitamin C to ba a dole bane sai an sha lemu sai a fake shan miyan kuka za ta wadatar.
Miyan kuka na kara kaifin basira, wannan wata hikima ce ta daban domin a hakika na kula da cewa mutanen da suke amfani da miyan kuka basirar su ta dara ta wadanda ba su amfani da ita. Nima na lura idan ina shan miyan kuka to karfin basira ta ya kan karu.
Kuka na dauke da sinadirran calcium fiye da wadanda ke a cikin madara.
Miyan kuka na wanke dattin ciki daga cushe-cushe, kusan ita kadai za ka sha ka konta kuma ka ta shi ka ji cikinka wasai ba kumburi ba tusa ba zafin ciki ba gudawa ba tashin zuciya, ba kaikayin jiki ko tsamin ciki. Ba kamar miyan kubewa ba ce wadda wasu idan suka sha kurajen jiki da kaikayi zai dame su.
Miyan kuka na taushe cututtukan ciki, ta magance kwayoyin cutar sanyi, ta karawa garkuwar jiki karfi dan samun damar yaki da kwayoyin cuta amma a nan za a rinka girkata da tafarnuwa da kuma daddawa.
Miyan kuka na samar da karfin kashin jiki a dalilinta na samuwar dimbin sinadiran calcium.
Miyan kuka kan rage taruwar kitsen tumbi ta kuma dai-daita matsayin sukari a jiki ta taimaka dan saurin narkar da abinci.
Miyan kuka na lausasa bayan gari mai tauri.
Miyan kuka na sanya wa jiki samun natsuwa da lafiyar ciki.
Bawan bishiyar kuka na maganin cututtukan fata, amma a nan mun takaita ga miyan ganyen bishiyar ne kawai.
Sai dai idan za a sha miyan kuka to bada kowane abinci ya dace ba duk da yake mafiyawan abinci kamar su shinkafa, masara, gero, dawa, duka rukunin carbohydrate ne sai dai kuma ta fi dacewa da wani abinci bisa ga wani.
Haka kuma idan za a girka ta to sai a daina cika mata kayan maiko da kayan yaji kamar tarugu da ko kuma kitse. A girka da daddawa da tafarnuwa ana kuma iya sanya man shanu. Allah ya taimake mu.
Comments
Post a Comment