Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR CIWON MARA YAYIN AL'ADAH.

 Yanda za a Magance Matsanancin ciwon Mara yayin Al'adah, da abubuwan dake haddasa warin gaba, da yadda za a Magance.


Budurwa ko matar aure me fama da wannan matsalar, zaki samu wadannan magungunan kamar haka;

- Garin hulba

- Garin habbatussauda

- Garin kustul Hindi


Saiki hadasu waje daya ki zuba ruwa da Zuma aciki sannan ki dafasu idan ya dafu saiki ajiye wannam ruwan da safe ki debi karamin kofi kisha kafin kici komai anaso ki dafa Wanda zai miki sati daya kafin ya kare kin huta da wannan matsalar insha Allahu
Abubuwan dake haddasa warin gaba

Ga Kadan daga cikin Abubuwan dakesa gaban mace yana wari.

1. Tafiya babu wando.

2. Rashin sanya takalmi, koda kuwa acikin gidane.

3. Dadewa akan masai (toilet).

4. Rashin canza pant da wuri.

5. Yawaita cin danyar albasa.

6. Istimna'i (Masturbation) wato mace ta

biyawa kanta buqata ta hanyar wasa da gabanta.

7. Tsarki da ruwan sanyi.

8. Rashin aske gaba, dadai sauransu.
Yadda za a Magance wannan matsalar

1. Ki dinga tsarki da ruwan dumi.

2. Ki dinga yawan canza wando a kullum kamar sau 2 ko 3.

3. Ki rage cin danyar Albasa.

4. Aduk lokacin da kika kama al ada ki dinga wanke gabanki da ganyen magarya da farin almiski.

5. Sannan ki daina tsugunawa akan masai (toilet) kina daukar tsawon lokaci.

6. Ki yawaita aske gabanta duk sati 1 ko 2.

7. Sannan kada ki rinka saka pant da jikar ruwa ajiki bayan kinyi tsarki ki goge kafin ki sashi

8. Kada kirinka barin iska tana shiga farjinki musamman matan Aure wasu suna kwanciya babu wando kuma panka ko a.c sunayi ki sani iska ko sanyi da wuri suke jawowa Mace illah a gabanta...

Comments