Main menu

Pages

ILLOLIN SAUYA FASALIN FATA DAGA BAKI ZUWA FARI GA LAFIYAR JIKI

 Illolin yin Canza fatar jiki daga baki Zuwa fari guda Tara (9) ga Lafiyar jiki; Binciken Masana

A Shekarar 2006, Hukumar FDA Food and Drug Administration da America, sun tabbatar kayayyakin da ake amfani dasu wajen bleaching basu da inganci ga lafiya.Binciken da akayi

Angano cewa"Kashi saba'in da biyar (75%) na matan nigeria suna bleaching, kuma a duk Africa sune na daya wajen bleaching.Kyayyakin da ake amfani dasu wajen yin bleaching 

- Sun hada da 

- Mai(Cream)

- Sabulu(Soap)

- Kwayoyi(whitening supplement)


Duk Kansu baka rasa sinadarai cikinsu irinsu:

Corticosteroid, Mercury, Hydroquinone. Duk suna haifar da illa a fata, da kuma sauran sassan halittun jiki(body organs).
Illolin su sun hada da;

1. Fata zata yi dabbare-dabbare

2. Jinkirin warkewa idan anyi rauni 

3. Matsalar koda(Kidney failure)

4. Yawaitar sinadarin PROTEIN cikin fitsari(PROTEINURIA) Wanda hakan babbar alama ce koda ta samu matsala

5. Kurajen fuska, kaikayin fata, Kurajen fata

6. Tabo

7. Matsaloli a jijiyoyin jiki, da hanta

8. Nakasu ga jariri idan aka yi bleaching ana dauke da cikin sa.

9. Blisters: Marurai dss.


Kowa ya tsaya yadda Allah Ya halicce shi yafi, fari ba shi ne kyau ba fa. Samari da 'yan mata a kula da kyau.Abun mamaki abun yayi yawa wallahi! Kaga yarinya baka kasanta, amma kaga tayi jajir lokaci guda bazato ba tsammani 
Sannan muma mazan da laifinmu wajen ba mata gudun mawa wajen yinsa domin dayawanmu cewa mukeyi munfi son mace fara. Shiyasa rana tsaka saikaga yarinya ta fara shafe shafe kan lokaci kadan tazama baturiya karfi da yaji 
Amma duk da haka Ku mata Ku kiyaye domin lafiya uwar jikice. Kitsaya inda Allah ya ajeki idan namiji yaga kin mishi ahaka ya aureki idan yaga baki mishiba yanemi wata Allah zai hadaki Dana gari mai tsoron Allah 

Comments