Main menu

Pages

HANYOYIN GYARAN JIKIN MATA GUDA GOMA, YADA ZAKI GYARA JIKINKI

 



Ire iren gyaran jiki na Mata har kala goma, yadda za a gyara jiki yayi kyau ba tare da Cutar da Fata ba.


Mafi yawan mata na son gyara jikinsu dan birge maigida ko kuma masoyan su, sai dai kuma akan samu akasi wajen yin amfani da abubuwan Turawa wanda suke da matsololi daban-daban sabanin yin amfani da abubuwan da ake da su na amfanin yau da kullum. 




Gyara ko tsafta abu ne mai matukar mahimmanci kuma abu ne me kyau muddin ba za a kauce wa addini ba. Hausawa na cewa “in kana da kyau ka kara da wanka” wannan dalilin ya sa wannan shafi ya yi duba da wasu abubuwan karuwa game da gyaran fata har ma da wasu abubuwan dan karuwar jama’a.


Tsarabar da wannan shafi yake dauke da ita ta hada da abubuwa kamar haka:


Macen da take son fatarta ta goge ta yi kyau za ta yi amfani da:

- Lemon Tsami 

- Bawon kwai 

- Kur-kur 


A hade su waje guda a daka su a runka wanka da shi, fata zata yi kyau yadda ake bukata.


Baya ga haka akwai hadi na musamman wanda in mace ta yi shi duk tsufanta za ta koma yarinya shakaf.


- Ayaba 

- Sabulun Salo 

- Man Auduga 

- Dudu Osun 

- Dettol 

- Leman Tsami 


Shi ma za a hada su waje guda a runka wanka da shi fata tana tsantsi da laushi.


Bayan haka akwai wani hadin na gyaran fata inda za a samu:


- Ganyen Magarya 

- Man zaitun 

- Man Habbatus sauda 


A daka ganyen magaryar a zuba a cikin man zaitun da man habbatus sauda a runka wanka da shi.


Hadi na musamman da yake sa fatar mace ta zamo tana tare da sheki, da laushi, har ma aji jikinta yana wani damshi-damshi sai a samu:


- Ayaba 

- Lemon Tsami 

- Tatacciyar Madara 

- Kwai guda daya.


A sami ayaba mai kyau a bare ko a matse da hannu, ko a markada yayi laushi, sai a zuba tacacciyar madarar a fasa kwai kamar guda daya, amma farin za’a zuba, sai a matse lemon tsami a gauraya shi a shafa a jiki ya samu kamar tsayin awa daya, sai ayi wanka da ruwan zafi. Idan ana yi kamar kwana uku za a sha mamaki Insha Allah


 


Gyaran fata na ban mamaki ki samu:

- Man zaitun 

- Ridi 


A daka ridi, amma sai an gyara shi, an shanya ya bushe sai a daka a zuba cikin man zaitun, idan za’a kwanta bacci sai a shafe fuska da jiki da safe sai a wanke za’a sha mamaki.


 


Idan kina son gyara kafar ki cikin sauki ki sami:

- Man Shanu 

- Man kwakwa 

- Man ridi 

- Man alayyadi.


Idan kafa na tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayukan guri guda a shafa a kafa in za’a kwanta bacci da daddare sai a daure da leda, da safe a wanke da ruwan dumi, a shafa man zaitun da man ridi.


 


Har ila yau idan ana so a gyara kafa za a samu:

- Man kwakwa 

- Man Shanu 

- Man Zaitun.


A hada man kwakwa da man zaitun guri guda, sai a shafe kafar da daddare, da safe a dan gasa kafar sannan a wanke, a shafa man zaitun.


 


Bayan wannan akwai wani hadin da za a samu:

- Ruwan Kokumba 

- Lalle 

- Man ridi


A hada ruwan kokumba da lalle guri guda, a shafa a kafa da safe a wanke, sai a shafa man ridi.


 


Idan mace nason rage kiba ko kuma tumbi musamman masu fama da kiba ko tumbi wannan hadin idan kika yi koda kina da kiba ba zai hanaki aikin komai ba kuma hadin zaisa ke da kanki ki sha mamaki.

- Garin hulba

- Ganyen Kanunfari

- Zuma

- Lemon Tsami

- Farin kwalli

- Man Na’a- Na’a


A hade wadannan ganyen guri guda a tafasa a sami farin kwalli dunkulen za’a sa ciki, idan ya kai kamar minti 5 sai a cire, sannan a saka zuma a cikin ruwan sha, a samu man na’a-na’a a rinka shafawa tumbin zai ragu insha Allah. Idan kuma ana son rage kiba ne za’a runka zuba lemon tsami a ciki. Allah Ya sa a dace.

Comments