Amfanin Shan Shayin Zobo da citta da Zuma guda goma Sha biyu (12).
Ka nemi citta bussashe qwara uku masu kyau ka hada da Jan so6o shima bussashe ka wanke sai ya wanku sai ka tafasa sai ya tafasa sosai, ka tsiyaye ruwan ga cup madaidaici sai ka tarfa Zuma cokali uku manya sai ka fifita sosai idan ya dan huce sai ka sha bayan an karya da kuma yamma bayan an ci abinci.
Wannan abun sha ne da yafi dukkanin kayan zaqin nan na kolba dana gwangwani da ake sha na drinks amfani nesa ba kusa ba.
Magunguna da wannan hadi keyi sun hada da;
- Kara jinin jiki fiye da kowane irin abinci da wani abun sha.
- Yana karawa jikin yara ,maza da mata harma da tsofaffi lafiya da kuzari zaka rinka jin kanka garau a koyaushe.
- Yana maganin cutukan huhu irin su tarin sanyi na mura, majina, tarin tibi, asma, tarin nimoniya da ciwon kirji, da kurajen huhu da majinar kirji da ta daskare,da tarin bronchitis.
- Yana wanke cikin da ya cushe saboda ciye ciye na kayan maiko da zaqi, yana magance kumburin ciki, tsutsar ciki, zafin ciki, yawan tusa, da yawan lalcewar ciki da tsutsar ciki da ciwon ciki, da yawan zuwa toilet,da sauran su.
- Yana maganin cutukan fitsari waton urinary tract infections, kamar yawan fitsari da jin zafi yayin fitsari,da fitsarin jini, da kaikaiyin matse matsi, da cutukan sanyi da sauransu
- Yana Maganin cutukan jini,da kumburin jini, da ciwon ga6o6i da jijiyoyin jiki waton joint and muscle pain.
- Yana maganin hauhawan jini da saukowar jini waton hypertension da kuma hypotension.
- Yana wanke babbar hanji da lausasa bayan gari mai tauri da rage radadin ciwon basir mai tsiro.
- Yana Maye gurbin karancin sinadarai masu samarwa jiki da isasshen jini.
- Yana karawa hanta lafiya da kare cutukan koda.
- Yana karawa masu HIV karfin jiki da kuzari kuma yana rage kaimin ciwon sida waton Aids.
- Yana sa kiba ga mata da maza masu sirrantaka na jiki da bana halitta ba.
A jarraba za ayi matukar jin dadin wannan maganin. Da fatar Allah ya sa mu amfana
Comments
Post a Comment