Main menu

Pages

AMFANIN SHAN KURKUM DA MADARA GUDA SHA BIYAR




Amfanin Shan Kurkum da Madara guda Sha biyar (15).

Kurkur a turance ana kiransa da Tumeric. Ana samun shi a kasuwanni da wajajen cibiyoyin Islamic medicine. Yana da amfani sosai ta 6angaren kiwon lafiya, rigafi da magance wasu daidaikun cutuka.




Za a nemi karamin cokali ayi amfani da shi, za a saka daya na garin tumeric sai a gauraya da rabin sachet ko sachet na madarar peak. za a yi haka ne a lokacin da ake da bukata da yin haka.



1.Yana kara karfin garkuwar jiki. Ta yanda jiki zai samu damar iya yaki da kwayoyin cuta da kuma baiwa jiki kariya daga barazanar kutsowar wasu abokan gaba.



2- Yana magance zafin jiki da yawan gumi.


3. Za a iya sha idan ana fuskantar barazanar kamuwa da ciwon daji waton cancer, sai a sha ba tare da an sanya madara ba.



3-Ana hadawa a baiwa yara su sha, dan karin karfin basira dana kwakwalwa.

4- Za a iya sha a sanda ake neman magance rashin samun isasshen bacci a jiki.


5. Magance yawan damuwa da rikirkicewar jiki.

6. ciwon jiki da kasala ga masu anemia.

6. Maganin yawan mantuwa.



7. Magance ciwon sugar amma kada a sha a tare da madara, kurkur din kawai za a sha da safe sai a dan motsa jiki har sai an yi gumi.



8-maganin kumburin wani sashe na jiki ko ga6a.

9. Yana maganin ciwon jiki na arthritis.

10. Magance cutukkan ciki.

11. Karawa fata armashi da lafiya.

12. Tace wasu sinadaran dake yiwa jiki lahani

13. Rage yawan hawan jini.

14. Rage tai6a.

15. Maganin ciwon kai da jiki



Ga wadanda madara ke sanyasu kornafi ko kumburin ciki sai su zan sha a tare da kirfa kawai.


Za a sha bayan an ci abinci sau daya. Allah Ya sa a dace.

Comments