Main menu

Pages

AMFANIN RAGE SHAN SUGAR GUDA TARA GA LAFIYAR JIKI

 



Amfanin rage Shan Sugar ko datse shi na sati biyu guda Tara ga Lafiyar jiki.


Da ace mutum zai fahimci irin illolin da sugar yake yi masa to tabbas da zai daina amfani dashi har abada kuma zai mai dashi cikin rukunin miyagun kwayoyi.



Amma gawasu alfanu da dan adam zai samu idan ya daina amfani da sugar tsawon sati biyu kadai.



1- Fuskar mutum zata canza zata rage kumburi zata danyi tsawo ta kara kyau dai dai misali. Mata ku kula da wannan sosai.



2- Datse sugar na tsawon sati biyu kadai zaisa idanunka/ki su kara samun lafiya sannan sukara da kyau da haske.



3 - Inganta lafiyar kwalwa da kara samun kaifin hankali da inganta tunani mai kyau.


4- za a rage yawan fita fitsari da daddare. Wannan shiyasa masu ciwon sugar ke fama da yawan jin fitsari akoda yaushe.


5 - Za a samu yawan karfi da inganci a kuzarin namiji da yawan ruwan sperm da karin Ni'ima ga mata.


6- Katse suga yana taimakawa wajen rage kumburin jiki da ciwon gabobi (inflammation) da sanransu.


7- Rage kiba


8- Samun Kyakkyawar fata, kuraje zasu mutu fatar fuska da ta jiki za tayi kyau, kyalli da santsi.


9- Daina amfani da sugar yana bada kariya daga kamuwa daga ciwon sugar.


Wallahu aalam.

Comments