Main menu

Pages

ALAMOMIN DA MACE ZATA GANE TANA DA NAMIJIN DARE (JINNUL ASHQ)

 Alamomin goma Sha daya da Mace zata gane cewa tana fama da Namijin dare (Jinnul Ashq).

Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar sune:-


Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita acikin barci, yawancin mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayi,bamma sai su dauka halin mafarkine kawai, to a gaskiya ba haka lamarin yake ba.
Yadda lamarin yake shine:-

Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin zaka sameta tana fama da wadannan matsalolin maka zakaji tace tana fama dasu.

Gasu kamar haka:-

[1] Bacin rai ba tare da anyi mata komaiba, haka kawai taji tanajin haushin kowa har ma mijinta, ko kuma taji kamar mijin nata ya saketa, ita ta gaji da auren,wanda da zaka tambayeta laifin mijin nata bazata iya fadin komaiba akai, kai wata rana ma taji ta tsani y'ay'an data haifa.[2] Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya jin magani ko kadan.


[3] Tsananin ciwon kirji da ciwon baya mai tsanani.


[4] Tsananin ciwon mara lokacin jinin al,ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, kuma tasan wannan ruwan ba al,adarta bane, ruwan kuma ya kasu kamar haka, akwai Mai yauki da marar yauki.

 Ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi

Ko fesowar kuraje masu zafi.[5] Idan mijinta yana saduwa da ita sai take jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita batajin zafi, amma bata samun biyan bukata.


[6] Gab da sallar magriba sai ta fara jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawa firgita,ko kasala da bacin rai.


[7] Idan ta dauki Al-Qur'ani zata karanta, saita rinkajin kasala, da hamma mai sanya hawaye, kuma tanajin barci sosai, amma da zarar ta ajiye Al-Qur,anin sai taji ta wartsake kamar ba itace takejin bacci dazun ba.


[8] Kuma idan ta kwanta zatayi barci sai ta kasa yin baccin tayi ta juyi akan katifa,idan mijinta yazo kusa da ita sai take jin firgici da tsoro.


[9] Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga zubewa ko ya canja ya zama jawur, lebenta kuma ya rinka bushewa ko yayi jawur.


[10] Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani, amma ba amosani bane.


[11] Yawan kaikayin kunne dana hanci kamar mura zata kamata, amma kuma ba mura bace,

Comments