Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE KAWO CIWON KUNNE DA YADDA ZA A MAGANCE SU

 Cikakken bayani akan ciwon kunne abubuwan dake kawo su da yadda za a Magance su.

Mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining ciwon tsakiyar kunne ne (Otitis media).Abubuwan dake kawo ciwon kunne.

Yana daga cikin abubuwan da suke kawo ciwon tsakiyar kunne :

1- kwayar cututtuka kamar su :

    a- bakteria

    b- virus

Amma mafi yawa bakteriya ne , wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. ( akwai hanyar da ta hadasu dama).
2- Ana samun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu kamar Burbushin Kura, Gashin mage da sauransu ( Allergies).
Alamomin ciwon kunne

1- Mutun zaiji kamar wani abu ya cika masa kunne .

2- Rashin ji sosai

3- Zubar da ruwa a kunne

4- Jin zafi a cikin kunne .

5- kaikayi

6- Zazzabi da ciwon kai .
Alakar Mura da kaikayin kunne

Gaskiya akwai alaka tsakanin mura da ciwon kunne, mafi yawan mura yana kama hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akwai hanyar da ta hada tsakanin Makogoro da Hanci dakuma tsakiyar kunne .
Kamar yadda mukace kwayoyin cutar bakteriya, da virus da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne.

To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro, hanci da kunne.Diga man Zaitun a matsayin Maganin ciwon kunne;

Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su gentamycin bai kamata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.Dalili shine wani lokocin ana samun hujewan dodon kunne (rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne  irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.Sahihin Maganin ciwon kunne :

Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya takawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment, hakanan wanda aka samu ta dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.
Da yawa daga cikin mutane idan kunnensu yana ciwo kawai zuwa suke chemist a wanke musu kunne.


Bincike ya nuna akwai sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana wasu kwayoyin cuta na bakteriya da makamantansu girma da shiga cikin kunne,  a garin wanke daudan kunne idan aka wanke wadannan sinadaran to daga nan anbudewa kwayoyin cuta kofa ne don haka sai a kiyaye wankin kunne .
Yawan kwakule daudar kunne

Amfanin "dauɗar kunne" da illar ƙwaƙwale ta.

"Dauɗar kunne" wani ruwa ne mai ɗan danko da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saɓanin yadda Bahaushe ke cewa "dauɗar kunne" ce . Saboda haka "dauɗar kunne" ba dauɗar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje. Allah da Ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan "dauɗar kunne", haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan "dauɗa" da kansa.
Daga cikin amfanin "dauɗar kunne" akwai:

1. Cafke dukkan nau'in ƙura, ƙasa, ƙwari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.

2.  Kashe kwayoyin bakteriya, da sauransu.Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:

1. Magogin kunne wato 'cotton bud' a turance.

2. Tsinken tsintsiya

3. Mirfin biro

4. Kan ashana

5. Gashin kaza, da makamantansu.


Sanya waɗannan abubuwa cikin kunne don ƙwaƙwalo "dauɗar kunne" na da haɗarin:


1. Ƙara cusa "dauɗar" zuwa can cikin kunne.

2. Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.

3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.

4. Raunata gangan kunne yayin da irin waɗannan abubuwa suka zarme cikin kunne.

5. Shafe ko manne "dauɗar kunnen" a kwararon kunne.
Haka nan, zira waɗannan abubuwa cikin kunne don susa ko ƙwaƙwalo "dauɗar" akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share ƙwararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baƙin abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.


Kada ka ɗauki ɗabi'ar sa  magogin kunne cikin kunne don goge "dauɗar kunne" kullum.

Comments