Main menu

Pages

ABUBUWAN DA MACE ZA TAYI DON MALLAKE ZUCIYAR MIJINTA

 Abubuwa guda hudu (4) da Matar Aure za tayi don Mallake zuciyar Mijinta.


A yayin da ake kulla alaka ta soyayya tsakanin mata da maza a koda wane lokaci, hakazalika aure wanda shine ribar kowace soyayya yana kasancewa idan alaka tayi karfi.
A wannan lokacin mun  kawo muku wasu sirrika musamman ga mata wajen rike miji a gidan aure da sai dai mutu ka raba idan ta kiyaye.
Duk macen da ta yi riko da wannan sirrika ta gama cin ribar aure da idan mijinta ya fara tarairayar ta wasu ka iya cewa ta asirce shi.
Mun kawo muku wannan sirrika da sanadin tuntuben mazaje dangane da irin dabi'u tare da halayyar macen da suke sha'awar zama da ita a matsayin matar su.Ga jerin sirrikan kamar haka:1. Tsafta: Tsafta tana daya daga cikin ababen da ya kamata kowace matar aure ta kiyaye domin ta kara neman tushen zama a zuciyar mijinta.2. Girmamawa tare da mutuntuwa: Ya kamata kowace matar aure ta girmama mijin ta, iyayen sa, abokan sa, da kuma dangin sa baki daya. Hakan zai kara dankon soyayya tsakanin ta da mijin ta.3. Sirri: Sirri yana daya daga cikin shikakai na aure, domin kuwa yana daya daga cikin ababe da ya kamata uwargida ta kiyaye wajen rufe asirin mai gidan ta ba tare da bayyana shi koda ga iyayen ta ba.4. Hakuri: Ginshikin kowane al'amari na rayuwa yana bayuwa ne ga hakuri, domin har ta ibadun da muke sai mun yi hakuri da juriya zamu iya dabbaka su. Hakazalika ana son mace ta kasance mai hakuri fiye da mijinta a yayin da take dakin mijin ta.

Comments