Main menu

Pages

YADDA ZA AYI AMFANI DA BAGARUWA WAJEN GYARAN JIKI.

 



Hanyoyi uku da za ayi da Bagaruwa wajen gyara jiki.


 Ana Amfani Da Bagaruwa Wajen Maganin quna Sakamakon yadda mu ke amfani da wuta yau da kullum, musamman ma matanmu, idan har aka samu tsautsayi aka kone, to za a iya amfani da bagaruwa don samun waraka daga kunan. 




1- Yadda mutum zai yi amfani da bagaruwa don samun waraka daga konewa shine, ya samu 'ya'yan bagaruwa da su ka bushe, sai ya daka 'ya'yan bagaruwar ya ke zubawa a wajen da ya kone din. Idan kuma bai samu busassun 'ya'yan bagaruwar ba, duk da haka zai iya amfani da danyen 'ya'yan.


 Ya samu danyun 'ya'yan bagaruwar ya ke matsa ruwansu akan kunan, zai samu waraka.





2. Ana Amfani Da Bagaruwa Don Samun Fararen Hakora Kuma Ma Su Haske.

Mu na kyautata zaton da mai karatu ya ga wannan kanun, hankalinsa zai koma kan sakamakon binciken masanan da mu ka kawo mu ku a sama, game da yadda bagaruwa ke samar da fararen hakora.




Don samun wannan fa'ida ta bagaruwa sai ka samun icen bagaruwa ka ke yin asawaki da shi, musamman ace ka daure ka ke yin aswaki da icen bagaruwar a kullum. Kuma zai fi kyau ka yi hakan sau biyu a kowacce rana, da dare kafin ka kwanta barci, sannan da safe bayan ka farka.




Hanya ta biyu da za a iya amfani da bagaruwa don samun fararen hakora ita ce, ka samu sassaken bagaruwa ka hada shi da jar kanwa ka jika, ka bar su su jika sosai, sai ka dinga kuskure bakinka da shi a kowacce rana, shi ma wannan an fi son ka yi hakan yayin da za ka kwanta da kuma bayan ka tashi daga barci.





3. Bagaruwa Na Samar Da Matsi Ga Mata

Matan da su ka amsa sunansu, ba sa yin sake da gyaran jikinsu don gamsar da mazajensu yayin ibadar aure. Mata za su iya amfani da bagaruwa don matse kansu. Yadda za su yi shine, su samu 'ya'yan bagaruwa da sassakenta sai su hada da Rihatul-hulbi su zuba cikin tukunya su dora kan wuta bayan sun zuba ruwa dai-dai misali.




Idan su ka tafasa sai su sauke sannan su tace su zuba shi cikin buta su dinga tsarki akai-akai. Idan maganar matsi ne, za ki bai wa kawarki labari, don kuwa wannan hadin bagaruwa na matse mace sosai.

Comments