Main menu

Pages

NAU'IN JININ DA IN MAI CIKI NA DASHI JARIRIN CIKINTA ZAI IYA HALAKA.

 


Cikakken bayani akan Wani nau'in Jinin in Mai ciki na da irinsa zai iya halaka Dan dake cikinta.

Mata masu ciki da ke dauke da jini nau'in "o-" kuma jaririn da ta ke dauke da shi jininsa "+" ne, hakan kan jefa rayuwarsa cikin hatsari, in ji likitoci.
Sai dai masu wannan nau'in jini ba su da yawa a duniya idan aka kwatanta su da masu nau'i mai "+" a duniya.
Mafiya yawan masu dauke da nau'in jini "-" dai, an fi samunsu a tsakanin fararen fata, inda suke da kashi 14 cikin dari.Yayin da a tsakanin 'yan Afrika kuma yawansu ya kai kashi shida cikin dari, sai yankin Asia da suke da kashi daya tak cikin dari.Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce ana yi wa kowace mace mai juna gwajin jini domin sanin irin nau'in jininta.Hakan a cewarta na taimakawa wajen sanin ko jininta ya bambanta da na 'dantayin da take dauke da shi.Idan jinin na su ya banbamta, hakan zai iya samun matsala, idan ba a dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba.


Hukumar ta ce an kasa jini zuwa manyan gidaje hudu wato A da B da AB da kuma O.


Sannan duka wadannan sun sake rabuwa zuwa gida bib-biyu ko positive wato wanda ake yi wa alamun tarawa ko kuma negative wato wanda shi kuma ake yiwa alamun debewa.

Saboda haka aka kara karkasa jinin zuwa nau'uka takwas.Sai dai hukumar ta ja hankali da cewa, idan za a yi wa mutum karin jini, kada a sa masa jinin da ba sa haduwa da nashi, domin yin hakan zai iya jefa rayuwarsa cikin hadari.A nan ta ba da misalin cewa, ba a kara wa mai jini nau'in "B" jin nau'in "A", ko kuma mai "A" a kara masa nau'in "B", domin sojojin dake baiwa jiki kariya dake cikin jinin za su yaki juna.Amma mai nau'in jini "O "zai iya bai wa kowa jini, saboda a cikin jininsa ba shi da antigens A ko B da zasu yaki na sauran nau'ukan jinin.Hukumar ta kara da cewa a mafiya yawancin lokuta ana yi wa mutanen da ke bukatar karin jinin gaggawa wadanda kuma ba a san irin nau'in jininsu ba, ana kara musu nau'in jini "O-".


NHS ta yi karin haske da cewa ana yin hakan ne saboda nau'in jini O- bashi da antigen A da B da RhD a kwayoyin halittar da ke cikinsa.


Sai dai mai wannan nau'i na (-) ba sa karbar kowane jini sai irin na su.

Comments