Main menu

Pages

ILLAR CIRE MA JARIRI HAKIN - WUYA KO DAN - WUYA, A LIKITANCE

 



Illar cire 'yar - wuya/ Hakin - Wuya ga Jariri da matsaloli shida da hakan ke haifarwa Jinjiri.


Al'adar cire 'yar-wuya ga jarirai wato "traditional uvulectomy" a turancin likita, daɗaɗɗiyar al'ada ce a ƙasar Hausa. Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa abin da Bahaushe ke cewa 'yar-uwa, wacce ke da sifar tsiro ko kuma kan yatsa, a can cikin baki daga sama, wani rumbu ne da ke ɗauke da ƙwayoyin garkuwar jiki domin yaƙar cutuka daban-daban.  Sai dai, al'adar Bahaushe ta gudana kan cire 'yar wuyan ga jarirai tsawon zamani, musamman a ƙasashen Hausa da kuma wasu ƙasashen Afirika. 




Malam Bahaushe dai yana ganin cewa 'yar-wuyan wani tsiro ne da zai iya cutar da  jariri yayin shayarwa ko kuma ya kawo ciwon maƙogaro can gaba. Sai dai, wannan al'ada ta yi baram-baram da binciken kiwon lafiya a yau, a maimakon haka ma, cire 'yar-wuyan na jefa lafiyar jariri cikin haɗura kamar haka:



1. Yi wa jariri wawan miki/rauni a ganɗa.

2. Ciwo tare da kumburi a ganɗa.

3. Ɓallewar jini, musamman ga jariran da kan zo da matsalar tsinkewar jini bayan rauni.



4. Shigar ƙwayoyin cutuka ta hanyar wuƙa ko askar da aka yi amfani da ita wajen cire 'yar-wuyan, ko kuma shigar ƙwayoyin cutuka cikin raunin da aka yi bayan cire 'yar-wuyan.



5. Shigar ƙwayar cuta mai janyo ƙamewa ko kakkafewar jiki, wato "tetanus" a turance, saboda haɗarin shigar cutar ta hanyar amfani da wuƙa ko aska mai tsatsa.


6. Matsalar shayarwa — saboda raunata hanƙa, jariri kan fuskanci wahalar haɗiyar nono yayin shayarwa.



Daga ƙarshe, likitoci sun tabbatar da cewa barin 'yar-wuya ba shi da wata matsala ga lafiyar jariri, kuma shi ne ma mafi alfanu ga lafiyar jariri. Kuma cire ta na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗuran da aka ambata a sama.

Comments