Main menu

Pages

DABI'U GUDA BIYAR DAKE RUGUZA SOYAYYAR NAMIJI A ZUCIYAR MACE

 



Wasu Dabi'u guda biyar dake taka rawa wajen ruguza soyayyar Namiji a zuciyar Mace.


1- Rashin Kula: Yawan lokacin da ka ba kowanne abu ke bayyana makomarsa. A misali, yawan lokacin da ka ke ba wa aikinka na bayyana yawan abinda zaka samu a karshe. Hakazalika soyayya kuwa, yawan lokacin da ka ba ta na nuna yadda za ta girma tare da habaka. Rashin kula kuwa na iya tarwatsa soyayyar namiji daga zuciyar mace.





2. Rashin Yabo: Mata na son a nuna musu idan har abu ya birge ko kuma sun yi dai-dai. Mata na son a yaba kwalliyarsu, girkinsu, maganarsu da sauransu. Rashin yabo na sa soyayyar namiji ta fita daga zuciyar Mace.





3. Kunci: Kunci na kawo rashin zaman lafiya a kowacce irin alaka. Ba soyayya kadai ba, hatta kawance babu mai son yi da mutum mai matukar kunci. Kunci na taka rawar gani wajen wargaza soyayyar namiji daga zuciyar Mace.




4. Kalubalanta akai-akai: Mata basu kaunar namiji mai yawan kalubalantar su. Kalubalanta na fara shiga tsakanin masoya ake samun babbar matsala tsakaninta da masoyinta.




5. Yi wa mace rikon sakainar kashi: Wasu mazan na soyayya da mace amma kiran mintoci kalilan na gagararsu. Wannan nuna halin ko in kula din na sa Mace ta daina son namiji kwata-kwata.


Akula dakyau mata sunada rauni kuma suna matukar son mai basu kulawa da wanda yadamu da damuwarsu.

Comments