Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANIN AMFANIN YIN ASUWAKI GA DAN ADAM

 
Amfani guda goma Sha biyar na yin Aswaki ga Lafiyar Dan Adam.


Aswaki nada asali tun ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W) wanda ya kasance sunnar sace na yin aswaki a kai akai a lokacin rayuwar shi wanda hakan yake yimana nuni ga yin aswaki na tattare da wasu hikimomi da kuma matukar muhimmanci ga lafiyar dan adam.
A yayinda ita kimiya sai tabi diddigin aswaki da kuma amfaninsa wanda daga karshe hukumar kiwon lafiya ta duniya(WHO) ta ayyana yin aswaki a matsayin abinda ke da amfani sosai ta fannin kiwon lafiya a wata takarda da suka wallafa a shekara ta 1986-2000 mai taken Oral Hygiene.
Amfani da aswaki a wannan zamanin naja baya inda wasu ke fifita yin brush fiye da yin aswaki ba tareda sanin cewa yin aswaki yafi amfani bisa ga yin brush ba.1. Aswaki na sanya karfin hakora da lafiyar baki da magance cutukan dake lailayi a cikin baki.


2. Aswaki na Fitarda dattin hakora  da maganin warin baki dama kurajen harshe.


3. Yin aswaki na maganin fitar jini daga hakora(gums bleeding)


4. Yin aswaki na kara armashin dandano (taste). Ta yanda idan kaci abinci zaka ji shi da dandanonsa kamar kada ka cinye.


5. Yin aswaki na maganin yawan ciwon kai.


6. Yin aswaki na sanya irin wani annuri ga fuskar mai yinsa.


7. Yin aswaki kan haskaka hakora musamman idan sun dushe musamman hakoran da suka dushe a sanadin shan taba ko cin goro ko shayi da dai sauransu.


8. Yin aswaki na karfafa gani


9. Yin aswaki na taimakawa abinci saurin narkewa.


10. Yin aswaki na gyara murya (clear the voice)


11. Yin aswaki na maganin nunfashi mai wari kamar na mai ciwon gyambon ciki. ko kana numfasawa amma kana jin wani wari na fitowa a cikin cikinka


12. Yin aswaki na maganin mugun tari


13. Yin aswaki na maganin ciwon hakora


14. Yin aswaki na magance dattin cin goro a hakora da warin hayakin taba.


15. Yin aswaki na kara lafiyar  ciki da cin abinci.


Allah Ya sa mu dage muyi tayin koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Comments