Main menu

Pages

AMFANIN ZAITUL LAWZ (ALMOND OIL) GUDA GOMA GA LAFIYAR JIKI

 



Amfanin Zaitul Lawz (Almond oil) guda goma a jikin Dan Adam.

Zaitul Lawz (almond oil) yana da amfani mai yawa ga jikin 'Dan Adam. Yana kunshe da sinadarai masu yawan gaske wadanda suke taimaka ma jikin 'Dan Adam. amma ga wasu kadan daga ciki:-


1. Zaitul Lawz yana maganin ciwukan da suka shafi zuciyar 'Dan Adam. domin yana kunshe da Sinadarin Folic Acid da kuma Potassium wadanda suke mutukar taimaka ma Kuzarin zuciya.




2. Yana maganin hawan jini, kuma yana zabgewa Cholesterol daga jikin mutum.




3. Mutumin da yake fama da matsalar kumburin ciki ko rashin narkewar abinci da wuri, idan yana amfani da ZAITUL LAWZ za'a dace.



4. Garkuwar jiki (AIDS, KANJAMAU)


5. Idan mutum yana fama da yawan mantuwar karatu, ko kuma rikicewar tunani, idan yayi amfani da Zaitul Lawz zai samu sauki.




6. Zaitul Lauz yana maganin tattarewar fata. Idan mutum fuskarsa tana saurin yamushewa ko kuma alamomin tsufa sun fara bayyana, da zarar ka fara shafa Zaitul Lawz zaka ga chanji na mamaki. Domin kuwa shi yana maganin yankwanewar fatar jikin Dan Adam.




7. Matan da suke fama da matsalar Karyewar gashi, idan suna shafa Zaitul Lawz zasu samu waraka. gashinsu zai yi karfi da sheki da laushi.



8. Zaitul Lawz yana taimaka ma jarirai wajen samun Qarfin hakora da kuma Qashin jikinsu.




9. Zaitul Lawz yana maganin Kaikayin jiki, ciwon jiki, da sauransu kuma yana taimaka ma gudanuwar jini a jikin Dan Adam.




10. idan mace tana sanya Zaitul Lawz acikin idanuwanta zasu washe suyi kyau sosai.


Anan zamu tsaya da fatan Allah ya amfanar da mu.

Comments