Main menu

Pages

ABUBUWAN DA AKESO MATA MASU CIKI SU DINGA AMFANI DA SU




Abubuwan da akeso Mata masu ciki su dinga amfani dasu domin inganta Lafiyar su da ta Dan dake ciki.

Anaso mata masu ciki surika amfani da Alkamah, kwai, ridi, waken soya, karas, da kuma zait zurra.

Yana kara masu lafiya, kuma koda mace tana lafiya kalau zata iya amfani dasu zasu gyara mata jiki sosai.




Ciwan gabbobi na masu ciki sai adinga tafasa Sha'ir anasha damadara. Kuma anaso ayawaita cin karas ko shan mansa, dayawan cin inabi, da gawasa, da kuma apple.



Haka idan ana yawan cin ya'yan baure, da ayaba, tafarnuwa, gyada, fasuliyya, to insha Allah idan kanacin wadannan itatuwan koda namiji ko mace to koda tsufa yazoma jikinka bazaiyi irin muguwar lalacewa dinnan ba insha Allah.




Ko asamo Ganyan Na'a Na'a da garin habbatisauda tarika tafasawa tanasha dazuma sau biyu arana, idan matsala tayi yawa sau uku arana.



Idan Mace tanada karamin ciki kuma tana fama da matsaloli to zata iya tarika tafasa ganyan Na'a Na'a dakuma Khal tuffa anasha to yana saukaka laulayin mata masu ciki insha Allah.




Bayan haka a tafasa ganyan Na'a Na'a da habba da zuma anasha yana kara ma mata masu ciki lafiya da ya'yan dasuke acikin nasu insha Allah.



Ko asamo man zaitun daman habbatisauda kowanne rabin lita ko lita dai dai masu kyau sai adinga shan cokali daya tare da zuma kafin akarya haka darana haka_ _dayamma kafin akwata. Zuwa wata shida, cokali bibiyu.



_Idan yakai wata Tara to cokali uku uku dasafe darana da yamma, haka itama zuman insha Allah zaa haihu lafiya.

Comments