Main menu

Pages

ZAZZAFAN MARTANIN 'YAN FILM AKAN MALAMIN DA YA KIRASU JAHILAI

 
Yan Film sun fusata suna mayar da martani  ga malamin daya kiransu da jahilai


Shima dai wannan malamin a kalamansa gaba daya bai taki gaskiya ba saboda idan kana bukatar a girmamaka yana da kyau kaima ka girmama al’umma wannan shine siradi na farko da malamai ya kamata subi domin samun masu karbar fatawar su.

Shidai wanna malamin gaba daya babu wanda yasan sa sai lokacin daya fara caccakar masu maulidi da kuma lokacin daya fara sukar yan kannywood hakika sunji ba dadi akan maganar daya fada musu inda ya kiransu da cewa dukkansu jahilaine babu wani mai ilmin addini.


Amma zuwa yanzu dole wannan malamin yayi nadama akan abinda ya aikata saboda yadda suka fito domin nuna masa cikakken kuskuransa ta irin yaren da yayi musu kuma da alama ba zaice komai ba amma kuma Hausawa nacewa wanzami baya son jarfa shin zai iya mayar da martani akai ko kuma zaija bakinsa yayi shiru.


Aganinku akwai lokacin kuwa dazai zo a samu jituwa tsakanin malamai da kuma yan kannywood saboda yadda ake ga miciji a Kullum basu da wata alaƙa mai kyau yan Film suna ganin malamai Hassada suke musu su kuma malami suna ganin yan Film suna bata tarbiya haka dai ake wannan zaman doya da manjan a tsakanin malamai da masana’antar kannywood.


Ga video ku kalla kuji yadda martanin ya kasance
Toni a nan sai ince Allah Ya ganar da wadanda suka kauce hanya.

Comments