Yadda za a Magance ciwon Ido kowane iri Insha Allah cikin sauki
Alhamdulillah Rabbil Alameen. Kamar yadda 'yan uwa suke yawan tambaya game da maganin ciwon "IDO" to a yau cikin yardar Allah ga wata fa'ida wacce idan mutum ya jarraba cikin yardar Allah kowanne irin ciwon ido ne Allah zai raba shi da shi.
Abinda za a nema;
1. Kwalli (Asmud/Ismudi).
2. Ruwan zam zam
Yadda Za a Hada
Da farko za a samu kwalli Asmud a bude shi sai a kawo ruwan zam zam a jika kwallin dashi, sai a barshi ya bushe idan ya bushe sai a rika sa abin sa kwalli ana sakawa a ido kullum yayin kwanciya barci.
Amma da farkon Sakawa zaka ji zafi kadan, amma daga baya zai zama babu zafi, kuma insha Allah idan kana saka shi na wani lokaci zaka ga sauyi da canji cikin yardar Allah.
Wallahu a'alamu.
Comments
Post a Comment