Main menu

Pages

YADDA ZA A SARRAFA GANYEN LANSIR DA TASIRIN DA YAKE A CIKIN JIKI

 Amfanin Lansir ga Lafiyar jiki da yadda za sarrafa shi

Lansir daya ne daga cikin ganyayyakin da wasu da yawa ke amfani da shi a fannoni da dama, musamman ma a tafasa shi a rika sha kamar Tea, ko a yayyanka ganyen a sanya a abinci arika ci da dai sauransu.

Wasu na amfani da shi ne kawai ba tare da sanin tarin amfanin da yake da shi a jikkunan da lafiyar mu ba. Tabbas Lansir abu ne da yakamata mu cigaba da amfani da shi, idan har kuma bamu taba amfani da shi ba, ya kamata mu fara amfani da shi saboda bincike ya tabbatar kuma ya nuna cewa: Yana da matukar amfani a jikin mu da kuma lafiyar mu.

Yadda ake yin amfani da shi

Za a samo ganyen lansir sai a wanke shi sosai a tsaftace shi sai a samo lemon tsami kadan a hada shi da ganyen Lansir ɗin, sai a zuba musu ruwa kofi 3 a ciki, a dora a kan wuta abarshi yakai mintuna 30 sai a sauke kuma a tace, sai a sha kofi 2, tsakanin shan kofi na farko da na 2 a bar tazarar akalla mintuna 15.

A samo ganyen Lansir sai a tsaftace shi a cire duk wani ganye wanda ba kore ba a jikinsa, sai a yayyanka shi a zuba masa ruwa kimanin kofi 2 sai a tafasa shi, idan yatafasa sai a sauke shi a barshi yayi mintuna 5 bayan ya huce sai a tace shi a rika shan kofi 1 kullum da safe kafin aci abinci.


A tsaftace kuma ayayyanka ganyen Lansir din sai a sanya shi a tafasa da ruwa, sai a barshi ya huce kuma a sanya shi a cikin wuri mai sanyi kamar frigde ta yadda zaiyi sanyi ba sosai ba, sai a rika shan kofi 1 da safe 1 da yamma.

Fa'idar Shan Wadannan Hade-Haden Na Lansir shine zai tsaftace maka Jini zai karama kuzari da kuma inganta lafiyar jinin jikinka baki daya

Comments