Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE AMOSANIN KAI, BAKI DA NA IDO GA MATA DA MAZA

 Yadda za a Magance Amosanin Kai, na Baki da na Ido ga Mace ko Namiji.


Abinda Ake nufi da Amodari ko Amosani;

Shine mutum ya dinga jin kaikayi a cikin kansa idan ya Sosa sai ya dinga jin dadi kuma ya dinga ganin wata kura ko gaari fari yana zubowa dags cikin kansa, shine amosanin kai kenan, malaman asibiti wato likitocin zamani sunce AMOSANI ba cuta bace halitta ce ta sa6a a shimfide a kan mutum saboda haka babu bukatar magani don ko anyi zai tafi ya dawo, amma mu a Islam ba haka bane gaskiya amosani cuta ce domin ba kowa ke da ita ba.

Illolin amosanin Kai

Amosanin kai kan sauka ya ratsa har idanun mutum ya sa idonsa kaikayi idan ka murza ko ka Sosa sai suyi jah kuma in yayi yawa ma yana ta6a ganin mutum yayi sanadiyyar makancewa Allah ya sawwake.
Amosani bai tsaya ga idanu kadai ba har cikin baki tsakankanin hakora ya sasu ciwo ko mutuwa yadda baza a iya tauna abu me Tauri ba, ko zubar hakora ko in anzo brush su dinga yin jini, ko kaji bakin mutum ko ya wanke sai bakin ya dinga doyi yana wari, in ya shiga cikin mutane sai a dinga toshe hanchi ana gudunsa saboda bakinsa na wari shi bai saniba. 
 Aure da dama ya mutu a Kan irin wannan matsalar ta amosani me sa warin baki ko warin farji ga mace har a dauka infection ne alhali amosani ne ya sauka mata tun daga kah har farjinta, Farjinta yayi ta wari kaman mushe in ba a gano bama sai a dauka ko sammu ko sihiri aka mata.

Amosani fa in yayi yawa har ga6o6in mutum yakan kama a dauka sanyin kashi ne ko ciwon ga6o6i Alhali Amosani ne ya yi yawa a jikinsa, kai har Mara kan kama ya Raunata gaban namiji a dauka ciwon sanyi ne in mace ce kuma  ya dauke sha'awa ayita maganin infection shuru ba waraka.
Alamomin Amosani

1. Kaikayin kai

2. Zubewar gashin kai ko rashin kyansa

3. Kaikayin ido

4. Ciwon hakora ko warin baki ko zubar jini in ana brush

5. Zubar farin garin kai e.t.c
Hanyar da za a Magance kowane irin Amosani

Za a tanadi abubuwa guda goma kamar haka;

1. Sabulun Salo Daidai Misali

2. Khal tuffah me hoton Apple guda 1

3. Man hulba Dan misrah guda 4

4. Garin Kaninfari cikin Babban Chokali uku

5. Garin bakin Gawayi na Hausa na Asalin Itacen Hausa banda gawayin zamanin nan me 6ako-6ako.


6. Zuma mekyau kuma a tabbatar zuma ce ba me hadi ba, ko Narkakken Siga da ruwa ba Pure Zuma ake so a kalla yawanta cikin Babban Chokali Biyar 5


7. Busashshen 6awon kwai

8. Man Kaninfari Dan Misrah guda daya 1

9. Ruwan zam-zam

10. Kwallin Ismudi
Yadda za ayi Maganin Amosanin Kai ga namiji

A aske kan gabadaya ayi malu sai a nemi khal tuffa me hoton Apple, da Man hulbah Dan misrah guda 4, in ka wanke kanka da sabulun salo da ruwan dumi sai ka bari ya bushe sai ka shafa ruwan khal din nan, shima in ya bushe sai ka shafe Kan da man hulba, haka zaka dinga yi safe da yamma kullum har zuwa fitowar wani gashin, inshaaAllahu ka rabu da amosanin kah kenan.
In Mace ce kuma sai ta Tsefe kan sai ta wanke kan da sabulun salo da ruwan dumi, idan Kan ya bushe sai ta shafa man hulba nan a cikin kan ba gashin kadai ba, domin AMOSANIN sa6a ce a cikin kanta a shinfide, in bata shafa a fatar Kan ba ta shafa a gashin kadai tayi aikin banza, sannan in tayi kitso ta dinga shafawa a kurmin kitson ma, haka zata yi tsawon sati biyu zata rabu da amosanin kah InshaaAllahu.

Maganin Amosanin Baki

Ka nemi garin Kaninfari chokali uku , ka kwa6ashi da zuma mekyau chokali 5, da garin Bakin gawayi mekyau da aka fada a baya, da kuma garin Busashshen 6awon kwai a dakashi ya dawo gari chokali biyu, da man kaninfari Dan misrah guda biyu, sai a hadesu da Zuman nan chokali biyar a kwa6esu, shine Maclean dinka/ki.
Sai a dinga dangwalar kwa6a66en kaninfarin nan kaman yadda ake dangwalar Maclean da Brush shima haka za a yi, sai ka goge bakinka sosai, sai a kurkure da ruwan dumi, sai ka kara kurkurewa da ruwan khal kuma, sai a bari sai bayan Mintuna biyar sai a kara kurkurewa da ruwan dumi again shikenan, ayi haka na sati biyu inshaaAllahu ka kashe Amosanin bakin gabadaya,
Me fama da matsalar warin baki ma kan iya amfani da wannan hadin amma ya dinga saka brush din har Kan harshensa yana gurzawa da brush din da ya dangwali maganin inshaaAllahu za a dace, haka me son tsaftar hakora ko haskensu zai iya yin haka ba sai me cutar AMOSANIN kadai ba. Hadin yana gyara hakora da karfinsu da haskensu, kuma ko ciwon hakori mutum yake ko kumburin desori ko kogo na hakori zai chiko kuma zai warke.
Maganin Amosanin Ido

A nemi Kwallin Ismudi a dinga sawa a idon da dare lokacin barci, sannan a nemi Ruwan zamzam a karanta fatiha kafa 7 a ciki sai a dinga digawa a cikin idon safe da yamma inshaaAllahu indai amosanin ido ne Allah zai yaye

Comments