Main menu

Pages

YADDA ZA AYI AMFANI DA SASSAƘEN KANYA WAJEN MAGANCE CUTUKA

 



Yadda Ake amfani da Sassaken Kanya wajen magance cutuka masu yawa.

Malaman tarihi suka Ce an yi ruwan dufana babu abinda ruwan bai halakar ba, duk bishiyoyin duniya saida suka mutu banda bishiya daya itace Bishiyar Kanya.

InshaaAllahu duk Ciwon duniya kanya na yi amma Banda mutuwa ko tsufa da yardar Allah!




Ba a sassako Bishiyar kanya kowacce rana Sai ranar da aka haifi Annabi Muhammadu S.A.W. Litinin (MONDAY) Kadai! Banda wannan ranar ba a sassakar kanya Sai wannan rana.

Duk itatuwan duniya babu Bishiyar da ta kai Bishiyar kanya tsufa a Duniya.





A sassako 6awon Bishiyar Kanya 6awon za a ganshi baki kuma a bushe, ana iya samunsa da datti, Sai a Dan wanke Sai a shanya ya tsantsame ruwan da aka jika shin, Sai kuma a daka shi Bayan ya bushe, Sai a tankade, in aka tankade ya zama kala biyu kenan;

1-Gari

2-Tsaki

Toh shi tsakin Sai an hada Masa mahadi, shi kuma Garin Daga lokacin ya shiga Aiki InshaaAllahu!




Me Ciwon ciki kowanne iri ne ya Debi garin ya zuba a ruwa ya sha ya warke har Abada InshaaAllahu!

Me fama da Ulcer ya kwaba garin da Zuma Yana sha chokali biyu da safe kafin ya Ci komi, biyu da rana Bayan cin Abinci, biyu da dare lokacin kwanciya tsawon kwana Uku a Jere InshaaAllahu ka rabu da Ulcer.




HAWANJINI

A nemi Zo6orodo/so6orodo/zo6o/so6o na yakuwa ka jika da ruwa, in ya jiku Sai ka tace ka Debi Kofi daya Sai ka barbada garin kanyar nan rabin chokali, Sai ka sha safe da yamma ka dinga yin haka kwana biyar ajere InshaaAllahu ka rabu da Hawanjini Har Abada cikin ikon Allah!





QABA WACCE TA SAKKO DA WACCE BATA SAKKO BA

Me fama da qaba ya Debi garin kanya chokali daya, ya matse lemon tsami guda Uku a cikin Zuma daidai misali sai ya rufe shi tun safe Sai dare Sai ya bude ya shanye InshaaAllahu zaiga Yana fitar da qabar kaman ruwan kabaiwa a fitsarinsa, ko da ya fitar da ita gabadaya ana son kar ya daina Sai yayi kwana Uku a Jere Yana yi, Bayan nan zai ga fatar marenansa ta yamutse sbd sa6ewar kumburin na Baya, toh Sai ya nemi man Shanu da garin kanyar Sai ya kwa6a ya dinga shafawa a gun kullum da dare in zai kwanta InshaaAllahu gun zai dawo kamar bai ta6a yin Qaba ba!




MATSALAR RAUNIN GABA

Nemi ruwa daidai yadda zaka iya shanyewa, sai ka karanta Qulhuwallahu kafa 7 ka tohfa a cikin ruwan, Sai ka Dan Debi garin kanyar nan Sai ka zuba a ciki ka kada Sai ka sha, InshaaAllahu Koda ya mutu ne Baya tashi cikin ikon Ubangiji zai mike!




ME CIWON HAKORI

Ya Debi garin kanya ya sa a gun InshaaAllahu zai daina har abada.




ME CIWON KAFA

Ya kwa6a Garin kanya da danyan manshanu sannan ya Dan diga kalanzir kadan Sai ya shafe kafar da dare in zai kwanta InshaaAllahu zai warke, haka Ciwon Baya, ko Paralyze a dinga shafawa kwana 7 a Jere InshaaAllahu an warke gabadaya.





MAITA/KUNGIYAR ASIRI/MIYAGU

A nemi kwarya a jika garin kanya chokali Uku a sha ludai daya amma ludayin duma, wallahi duk Wanda ya sha har abada maye ko Dan kungiyar asiri bazai ga kurwarsa ba bare ya kamashi har abada InshaaAllahu!




ME BASUR: ya dinga zuba garin a ruwa Yana sha safe da yamma kwana Uku an warke gabadaya InshaaAllahu!





YADDA ZA A YI DA TSAKIN KUMA:

A yanko ganyen kuka a daka a tankade Sai a hada tsakin kuka da tsakin kanya a dinga hayaki da shi a Jiki ko a tsakar Gida Yana kone aljanu da Kore mayu. Me fama da farfadiya a Masa alwala a Masa bayanin InshaaAllahu ya daina faduwa, haka me Ciwon Hauka shima a dinga Masa bayanin Bayan yayi alwala InshaaAllahu zai warke!




WANDA YAKE TUNANIN KO AN MASA SAMMU

A rubuta falaqi da nasi kafa daidai, Sai a sa garin kanya a cikin rubutun Sai bari Sai dare Sai ya sha ya shafe jikinsa InshaaAllahu take sammun zai kone.





FITSARIN KWANCE KOWANNE IRI NE

A nemi kaikayin gero Sai a jika da ruwa Sai ya kwana Sai a tace Sai a zuba garin kanya chokali guda, duk yawan ruwan kar garin kanyar ya wuce chokali daya, Sai a juye a cikin ruwan a gauraya Sai a bawa Yaro ludayi daya, duk yawan yaran ludai dai dai za a basu kowa, InshaaAllahu har abada sun daina Fitsarin Kwance.





MATSALAR RASHIN HAIHUWA

A samu kwan zabo ko na kazar hausa guda 6, Sai a FASA guda 2 a kada tare da garin kanya Rabin chokali, kuma a sa gishiri Sai a soya da mai Sai a cinye, haka za a yi ta yi tsawon kwana Uku a Jere kullum kwai shida sun kare kenan, InshaaAllahu kafin watan ya mutu Sai an sami CIKIN, in Namiji ne ke da matsala shi zai Ci, in mace Ce ke da matsala Ita zata Ci.

Comments