Main menu

Pages

KO KIN SAN YADDA ZAKIYI AMFANI DA BAURE WAJEN GYARA GASHI

 Yadda za kiyi amfani da Baure wajen gyaran gashi, yayi tsawo, Baki da sheki.


Baure itaciya ce mai matukar amfani ga dan adam tun daga diyan, sassaken harda ganyen ana sarrafasu domin magungunan mata da maza.


Amfani da baure wajen gyaran gashi yana da matukar alfanu kamar yadda yake dashi ga jikin mu.


Baure yana dauke da sinadaran vitamin v12, vitamin A da kuma sauran wasu sunadarai da suke tasiri sosai wajen inganta lafiyar gashi.

Suna taimakawa wajen girman gashi , kara mashi baki sannan suna kara mashi laushi da kyau da sheki.
Yadda za a sarrafa shi wajen gyaran gashi

(1) Za a samu baure guda biyu

(2) kwai daya

(3) cokali daya na zuma 

(4) cokali biyu na yoghurt


Dukkan wadannan sunadarai za a hadesu waje daya akwaba sai a sanya a gashi a murza ko ina. Bayan awa daya sai awanke da shampoo indai ana haka insha Allah za a samu biyan bukata .
HANYA TA BIYU

Asamu baure hudu ko biyar azuba cikin ruwa ya kwana dasafe acinye bauren ruwan kuma a zuba zuma cokali daya sai a wanke gashi da ruwan bayan yabushe asamu ruwa mai kyau awanke gashin insha Allah za a ga canji. Allah yabamu dacewa baki daya.

Comments