Main menu

Pages

HANYOYIN DA ZA A BI DON MAGANCE CIWON KAI MAI TSANANI

 Yadda Za a Magance Ciwon Kai Mai Tsanani cikin yaddar Allah

Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.


Ciwon kai yana daga cikin cutukan da ake fama dasu yau da kullum. Kuma yana da dalilai ko Musabbabai da yawa. Amma ga wasu fa'idodi masu albarka ka jarraba. In sha Allahu zaka dace :

1. Suratul Fatiha : Malaman Musulunci sun ce lallai fatiha tana maganin kowacce irin cuta ajikin 'Dan Adam. Yadda zakayi amfani da ita domin magance matsalar ciwon kai shine: Kayi Basmalah ka sanya hannunka na dama ka rike goshinka ko kuma wajen da yafi ciwon. ka karanta Fatiha Qafa daya sannan ka saki kan naka. In sha Allahu zaka ji ya dena.


Idan bai dena ba, ka sake rikewa sannan ka karanta Fatiha din Qafa uku. Zaka ji ya dena. Idan kuma bai dena ba, ka karanta Qafa biyar. idan bai dena ba, ka karanta Qafa bakwai. In Allah ya yarda zakaji ka warke nan take.

2. Man Habbatussauda: Ka samu Man Habbatus Sauda ka zuba acikin Garwashi sannan ka rika shekar hayakin. In sha Allahu zakaji babu ciwon kan.

3. Man Tafarnuwa, Man Gelo : Kowannensu idan ka shafa zaka samu waraka daga ciwon kan Insha Allah.


Allah Yasa mu dace.

Comments