Main menu

Pages

HANYOYI GUDA BIYU DA ZAKI BI WAJEN GYARAN GASHI YAYI TSAWO DA BAKI

 



Hanyoyi guda biyu kacal da Zaki bi don samun tsawon gashi laushi da baki.

Hanyoyi guda biyu da kowacce mace zatabi ta samu tsayin gashi da laushi da baki duka ba tareda tayi amfanida maganin bature ba,



 1- Abu na farko shine amfani da tafarnuwa da man zaitun yanda zakiyi saiki samu tafarnuwan da dan yawa kamar sama da goma saiki baresu ki yanyanka sannan ki jikasu da man zaitun saiki bari yayi kwana uku ajike saiki soya ki ajiye kina shafawa akai bayan sa'a daya (1hour) awanke.





2- Sai kuma na biyu shine amfani da man amla da man kwakwa da zuma yanda akeyi shine zaki zuba man amla kadan zuma itama idan amla ya zama cokali4 to zuma ya zama zuma cokali2 man kwakwa shima cokali2 saiki zuba a ruwan zafi shi kuma kamar cokali4 a gauraya kamar idan za'ayi shampoo sai ashafa akai bayan mintuna talatin (30minutes) shikenan sai kiyi shampoo dinki wato wanke Kai.

Comments