Main menu

Pages

GYARAN DA YA KAMATA MACE TAYI FARA BAYAN TA HAIHU DA SATI BIYU

 Gyaran da ya kamata Mace ta fara bayan sati biyu da haihuwa da Wanda zata fara daga ranar da ta haihu

 Abinda ya kamata kiyi bayan kin haihu da sati biyu sai ki fara shirya jikinki don tarbar maigida , don in dai lafiya kika haihu daga lokacin zaki tsinci kanki cikin kuzari.

Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba.

Don haka tunda tafiyar ta samu sai a fara shirya jiki, kiyi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki Fara ci, cin kazar yana Kara gyaran kasan mace ta zama zam- zam kamar bata haihu ba.
 

- Shan ya' yan itatuwa akai - akai baran ma ( kankana, abarba, gwada, lemon Zaki da sauran kayan fruits)
- Ki dinga yin Kunun aya kina sha. In zai samu Kiyi kullum, Amma karki dinga zuba sukari Dan kadan Zaki dinga sawa ko ki sha haka.
- shan maganin Mata mai kyau ( habbatus- sauda , Zuma , dabino , aya ,madara , nono Amma me kyau.


- Shan Zuma, madi, tsimi da sauransu.


-  Tun daga ranar da kika haihu har zuwa lokacin da zaki yi arba' in ki zama cikin tsaftace jiki da gyaran jiki, gyaran jariri, gyaran gida.
Kar kiyi sake da yin Turaren wuta na gida, da na jiki,

Don wasu matan idan suka haihu sai kaganta ( ragajab ba tsaftace jiki ) ko ina su a ganin su idan Ana jego ba a gyaran jiki tunda mijinta Baya tare da su a shimfida , kana zuwa kusa dasu sai kaji wari da karni, wanda a musulinci ko yau mace ta haihu jini ya dauke Mata a ranar data haihu, mijinta yana da ikon zuwa ya sadu da ita a Ranar .

Comments